Kiwon Lafiya: Wai an gano maganin kanjamau a Najeriya

Kiwon Lafiya: Wai an gano maganin kanjamau a Najeriya

- Cutar Kanjamau wata kwayar virus ce mai zuwa ta kashe garkuwar jikin mutum daga cutuka

- Cutukan da kan shiga jiki a da amma jini ya yake su sai su kashe mutum

- Ya zuwa yanzu dai bata da magani, amma wasu a kasashe kan ce sun gano maganinta

Kiwon Lafiya: Wai an gano maganin kanjamau a Najeriya
Kiwon Lafiya: Wai an gano maganin kanjamau a Najeriya

A can kasar Chana, wasu likitoci a jami’ar gudanar da bincike dake Pokfulam dake Hong Kong sun bayyana cewa sun gano maganin warkar da kanjamau mai suna ‘Bi-specific Broadly Neutralising Antibody (bNAb)’.

Likitocin sun furta haka ne bayan sun yi gwajin ingancin wannan maganin a jikin wasu beraye dake dauke da cutar. Gaba dayan su duk sun war ke ta-tas.

‘‘Berayen sun warke ta-tas daga cutar kanjamau gaba daya bayan da muka yi amfani da wannan maganin a jikin su’’.

A karshe likitocin sun ce kara inganta wannan maganin zai zama maganin kawar da ciwon kanjamau na farko da aka sarrafa a kasar Hong Kong sannan kuma zai taimaka wajen kawar da cutar a duniya.

DUBA WANNAN: Sojin Amurka a NAjeriya?

A da dai, an sha gwada magunguna da ke dakatar da galabaitar masu dauke da cutar, amma kuma daga karshe sai jikin nasu ya kasa.

Sai da Amurka ta sami damar hada wasu hadakar magunguna da ake kira ARV, watau Anti-retro-Viral, sannan aka sami wata hanya da za'a hana cutar zame wa daga HIV ta zama AIDS.

Ita HIV ita ce kwayar cutar har zuwa shhigarta jini. Ita kuwa AIDS shine kamuwar da cutar ke yi ga jini bayan ta illata jiki da garkuwarsa.

Ana taron kwayar cutar da magani ne kafin ta iya lahanta garkuwas, amma muddin ta zama AIDS, sai la-haula.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel