Kotun Kolin Najeriya Ta Dawo da Batun Mawakin Kano da Ya Taba Mutuncin Annabi SAW
- An daukaka kara a hukuncin da aka yanke wa mawakin Kano, Yahaya Sherif Aminu kan taba mutuncin Manzon Allah SAW
- Kotun Koli ta fara sauraron shari'ar yau Alhamis, 25 ga watan Satumba, 2025, inda lauyoyin mawakin ke fatan samun nasara
- Tun a shekarar 2020, Kotun Shari'ar Musulunci a Kano ta yanke wa mawakin hukuncin kisa, amma daga baya babbar kotu ta soke
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kotun Koli ta fara sauraron shari’ar batanci da ake tuhumar wani mawaki dan kano, Yahaya Sharif Aminu da taba mutuncin Annabi Muhammad SAW.
Lauyoyin da suka daukaka kara domin kare wanda ake tuhuma sun bayyana cewa suna fatan hukuncin da kotun Koli za ta yanke zai takaita aiwatar da dokar shari’a.

Source: Facebook
Channels tv ta ce a 2020, wata kotun shari’a a jihar Kano ta yanke wa Yahaya Sharif-Aminu, hukuncin kisa kan wasu baitocin waka da aka ce sun taba mutuncin Fiyayyen Halitta (SAW).

Kara karanta wannan
Sanata Uba na neman jefa kansa a gagarumar matsala kan badakalar Naira miliyan 400
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka, Babbar Kotun Jihar Kano ta soke hukuncin, ta kuma bayar da umarnin sake shari’ar daga farko, matakin da lauyoyinsa ke ƙoƙarin dakatarwa.
Batanci: An dawo da shari'ar mawakin Kano
Lauyoyin mawakin sun garzaya kotun koli, inda suka nemi ta yi nazari kan hukuncin kisa da shari'ar musulunci ta tanada ga duk wanda ya yi batanci ko zina fa aure.
Daya daga cikin lauyoyin mawakin, Kola Alapinni ya ce:
“Bai kamata mu ci gaba da amfani da hukunce-hukuncen shari’a da suka saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokokin ƙasa da ƙasa da Najeriya ta amince da su ba.”
A halin yanzu dai Kotun Kolin Najeriya ta bai wa lauyoyin mawakin da ake zargi da batanci karin lokaci domin su gabatar da korafinsu.
Ana kokaren mawakin da ya taba Annabi
Duk da babu wani addini da gwamnatin Najeriya ta karkata a kansa, amma dokar shari’a tana aiki a jihohi 12 na Arewacin ƙasar da yawancinsu Musulmi ne.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano za ta dauki mataki kan malamin da ake zargi da taba mutuncin Manzon Allah SAW
Tun da aka fara wannan shari’a a kotuna zuwa Kotun Koli, kungiyoyin kare ‘yancin ɗan adam daga Amurka, Tarayyar Turai, da Majalisar Dinkin Duniya sun nuna goyon baya ga Sharif-Aminu.
A watan Afrilu, Kotun Ƙungiyar ECOWAS ta bayyana hukuncin kisa da jihar Kano ta yanke kan batanci a matsayin “mai tsanani kuma bai dace ba.”

Source: Getty Images
Kalaman batanci da Yahaya Sherif ya fada
Ana zargin Mawaki Sharif-Aminu da wallafa wasu baitocin waka a WhatsApp, inda ya ce wani shehunsa da yake bi yafi Annabi Muhammadu (SAW) daraja.
Lamido Abba Sorondinki, lauyan gwamnatin jihar Kano, ya shaida wa manema labarai cewa: “Duk wanda ya faɗi kalma da ta taɓa mutuncin Annabi (SAW), za mu hukunta shi.”
Amma Alapinni, da ke tsaye kusa da shi, ya yi dariya yana cewa: “Abokina lauya ba shi ne Kotun Koli ba, kawai yana kare wani bangare ne.”
An yi zanga-zanga kan zargin batanci a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wasu gungun matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano kan zargin da suke yi wa Sheikh Lawal Triumph na batanci ga Annabi SAW.
Gwamnatin jihar Kano bayyana cewa za ta iya daukar matakin shari'a kan fitaccen malamin addinin musuluncin.
Gwamna Abba ya shaida wa masu zanga-zangar su rubuto korafinsu a hukumance domin da shi za a yi amfani har zuwa kotun koli.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
