Shettima Ya Kalli Shugabannin Duniya, Ya Fadi Matsayar Najeriya kan Kafa Kasar Falasdinawa
- Najeriya ta goyi bayan kiraye-kirayen da Birtaniya, Faransa da wasu kasashe ke yi na kafa kasar Falasdinawa a Gabas ta Tsakiya
- Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana matsayar Najeriya a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a Amurka
- Sanata Shettima, wanda ya wakilci Bola Tinubu, ya ce kafa kasar Falasdinu za ta kawo karshen rikicin Falasdinawa da Isra'ila
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya na goyon bayan kasashen da suka amince da kafa kasar Falasdinawa.
Bola Tinubu ya yi kira tare da goyon bayan matsayar Birtaniya, Faransa, Kanada, Australia, Portugal da wasu ƙasashe wajen neman a amince da Ƙasar Falasɗinu.

Source: Twitter
Shettima ya gabatar da jawabin Tinubu a UNGA
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 da aka gudanar a birnin New York na Amurka, in ji Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada cewa mafita ta kafa ƙasashe biyu ita ce hanya mafi kyau wajen kawo ƙarshen dogon rikicin da ke tsakanin Falasɗinawa da Isra’ila a Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu Firaministan Isra'ila da Shugaban Amurka, Donald Trump ba su amince da bukatar samar da kasar Falasdinu ba.
A ranar Talata, Trump da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun bayyana ra’ayoyi mabambanta a kan batun kafa ƙasar Falasɗinu yayin wata tattaunawa a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya.
Sai dai a nasa jawabin wanda mataimakinsa, Kashim Shettima, ya karanta, Shugaba Tinubu ya goyi bayan kafa Falasɗinu a matsayin kasar Falasdinawa.
Najeriya ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu
Ya kuma soki yadda Majalisar Dinkin Duniya ke tafiyar da lamarin rikice-rikicen da suka haddasa take hakkin dan adama a Gabas ta Tsakiya da sauran sassan duniya, cewar rahoton Daily Trust.
Shugaba Tinubu ya ce:

Kara karanta wannan
"A tsage biri har wutsiya": Lauya ya nemi bayani a kan kudin da Remi Tinubu ta tara
“Muna faɗa ba tare da boye-biye ko shakka ba cewa samar da ƙasashe biyu ita ce mafitar da za ta kawo zaman lafiya mai ɗorewa ga al’ummar Falasɗinu.”
“Falasɗinawa ba kaskantu ba ne, su ma mutane ne kamar kowa, masu daraja iri ɗaya, wadanda suka cancanci ‘yanci da mutunci kamar yadda kowa ke da shi."

Source: Twitter
An fara sukar Majalisar Dinkin Duniya
Wasu ƙasashe sun nuna damuwa kan yadda Majalisar Dinkin Duniya ke jinkirin ɗaukar matakai saboda tsarin veto, wanda ya sa aka kasa cimma matsaya a rikice-rikicen Gaza da Ukraine.
Hakan ya sa ƙasashen duniya suka fara ganin cewa Majalisar Dinkin Duniya na ƙara rasa damar iya kare rayukan fararen hula da kuma dakatar da gaza ladabtar da masu aikata laifuffuka.
Trump ya ji haushin abin da ya faru a UNGA
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana damuwarsa kan matsalolin da ya fuskanta a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a New York.
Shugaba Trump ya ce daya daga cikin abubuwan da ya fuskanta a taron wanda bai ji dadi ba shi ne yadda wata na'ura ta tsaya cak lokacin da shi da matarsa suka zo wucewa.
Donald Trump ya bukaci a gudanar da bincike kan duka matsalolin da ya fuskanta a lokacin da ya halarci taron kuma a dauki mataki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

