Atiku Zai Fifita Fulani idan Ya Samu Mulki? Wazirin Adamawa Ya Kare Kansa ga Yarbawa

Atiku Zai Fifita Fulani idan Ya Samu Mulki? Wazirin Adamawa Ya Kare Kansa ga Yarbawa

  • Alhaji Atiku Abubakar ya ce yana da alaka ta jini da Yarbawa tun daga aurensa da Titi, ’yar Ijesha, wacce ta haifa masa ’ya’ya hudu
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne matsayin martani ga masu cewa zai fifita Fulani idan ya zama shugaban kasa
  • Atiku Abububakar ya ce Yarbawa za su zama a sahun gaba a lamuran gwamnatinsa idan Allah ya ba shi nasara a zaben 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar wa Yarbawa cewa muradunsu za su kasance a sahun gaba idan ya zama shugaban kasa a 2027.

Atiku, wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya ce tsoron da ake yi cewa zai fifita Fulani idan ya hau mulki ba shi da gaskiyya balle tushe.

Kara karanta wannan

'Najeriya ba Legas ba ce,' ADC ta fadi abin da ke shirin faruwa da Tinubu a 2027

Atiku Abubakar ya ce ba gaskiya ba ne cewa zai fifita Fulani idan ya zama shugaban kasa.
Alhaji Atiku Abubakar yana daga wa masoyansa baya a wani gangamin PDP da aka gudanar. Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku Abubakar zai ba Yarbawa fifiko

A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Kola Johnson, ya fitar, Atiku ya ce dangantakarsa da Yarbawa ta samo asali tun daga aurensa da Titi, ’yar Ijesha, a 1970s, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya ce:

“Na yi matukar sa’a ta samun aure daga wannan kabilar mai daraja, kuma hakan ya kafa zumunci irin na jini tsakanina da Yarbawa. Wannan ne ya sa Yarbawa kullum suna da matsayi na musamman a zuciyata.”

Atiku ya jaddada cewa matarsa Titi, wacce yanzu tana da sama da shekara 75, ta haifa masa ’ya’ya hudu Yarbawa, kuma suna kiransa Baba Rere ma’ana uban kirki.

Ya ce yana alfahari da kasancewarta matarsa da kuma irin rawar da ta taka wajen kulla dangantakarsa da Yarbawa tun shekaru da dama da suka wuce.

Atiku ya karyata zargin fifita Fulani

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce Yarbawa za su kasance a gaba a duk wata manufa ko shirin gwamnati idan Allah ya ba shi nasarar zama shugaban kasa a 2027.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya shawarci Atiku Peter Obi kan takara da Tinubu a 2027

Atiku Abubakar ya ce:

“Saboda haka, maganar cewa zan fifita Fulani a kan Yarbawa ba ta taso ba, domin Yarbawa sun riga sun zama ’yan uwana da iyalai na jini.”

Atiku ya ce koda kafin ya shiga siyasa, yana mu’amala da kowa ba tare da wariya ba, a cewar rahoton jaridar Tribune.

Atiku Abubakar ya ce idan ya ci zabe, zai ba Yarbawa fifiko
Alhaji Atiku Abubakar, lokacin da ya lashe zaben fiyat da gwani na PDP na 2022. Hoto: @atiku
Source: Facebook

'Yarbawa na da muhimmanci' - Atiku

Ya bayyana Titi a matsayin “wata zinariya mai matukar daraja” tare da jaddada cewa Yarbawa sun kasance abokan siyasa da kuma na kusa da shi tun da dadewa.

Ya kara da cewa Yarbawa suna taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, musamman wajen samar da daidaito a tsakanin Arewa da Kudu.

Atiku ya kasance dan takarar shugaban kasa na dogon lokaci, wanda ya tsaya takara karkashin jam'iyyu daban daban tun daga shekarun 1990s, har zuwa 2023, da ya zo na biyu bayan Bola Tinubu na jam’iyyar APC.

Titi na son zama uwargidan shugaban kasa

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Titi Atiku Abubakar ta ce tana so ta zama uwargidan shugaban kasa bayarbiya ta farko tun bayan dawowar damokuradiyya.

A wancan lokacin, uwargidar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ta ce har yanzu mutanen Kudu maso Yamma ba su samar da matar shugaban kasa ba kuma ita za ta rusa tarihin.

A cewar Titi, ya kamata dukkanin Yarbawan Najeriya su marawa takarar mijinta baya domin bata damar cimma burinta da kuma kara karfafa kabilarsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com