Dama Ta Samu: Gwamna Zai ba Malaman Sakandare Rancen N569m Su Sayi Mota da Gida
- Gwamna Biodun Oyebanji ya amince da bayar da rancen N596.6m ga malamai da ma’aikatan makarantun sakandare a Ekiti
- Babban sakataren hukumar kula da malaman sakandare, Michael Boluwade, ya ce rancen kudin na sayen motoci da gidaje ne
- A gefe guda, Gwamna Oyebanji ya riga ya amince da sakin N200m a matsayin rancen sayen gidaje da motoci ga malaman firamaren jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - Malaman makarantun sakandare na cikin alheri dumu-dumu yayin da gwamnan Ekiti ya amince a ba su rancen Naira miliyan 596.6.
Gwamna Biodun Oyebanji ya amince a ba malamai da ma'aikatan da ba malamai ba, su 807 rancen kudin don su sayi motoci da gidaje.

Source: Twitter
Ekiti: Za a ba malamai rancen N596.6m
Babban sakataren hukumar kula da malamai ta jihar Ekiti, Michael Boluwade ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya fitar ranar Talata a Ado Ekiti, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Michael Boluwade, ba da rancen kudin na daga cikin kokarin Gwamna Oyebanji na inganta walwalar malaman sakandare da firamare na gwamnati.
Sanarwar ta ce:
"Daga cikin kudin da aka amince a raba, an ware N381.5m domin ba mutane 382 rance don su sayi motoci, sannan an ba mutane 425 rancen N215.1m don su sayi gidaje.
"Za a raba wannan kudin ga malamai da ma'aikatan da ba malamai ba da ke aiki a makarantun sakandare, bisa ga umarnin gwamna na karin da aka samu."
Babban sakataren ya jinjinawa Gwamna Oyebanji bisa amincewa da fitar da kudin ga asusun ba da lamuni na hukumar, wanda zai sa a rabawa masu cin gajiya da wuri.
Gwamna ya fara cika alkawari ga ma'aikata
Ya shawarci wadanda za su amfana da rancen da su yi amfani da kudin bisa ga abin da suka nema, yana mai tunatar a su cewa za su biya bashin ne ta hanyar cire wani bangare na albashinsu.
Idan za a iya tunawa, Gwamna Oyebanji, a ranar ma'aikata ta 2025, ya ce gwamantinsa ta kaddamar da shirye-shiryen da za su inganta walwalar ma'aikata.
Ya lissafa shirye-shiryen da suka had ada ba da rancen N400m na sayen motoci da gidaje ga malamai da ma'aikatan da ba malamai ba, har su 1447.

Source: Original
Wannan na zuwa ne yayin da Gwamna Oyebanji, ya amince da sakin N200m domin ba da rancen sayen motoci da gidaje ga malaman firamare a jihar.
Wannan mataki ya cika alkawarin gwamnan na tabbatar da cewa malaman firamare na gwamnati sun fara cin moriyar wasu shirye-shirye da takwarorinsu dake koyarwa a makarantun sakandare ke ci.
Wata sanarwa da aka wallafa shafin gwamnatin Ekiti na intanet ya nuna cewa an riga an tura N50m zuwa asusun masu cin gajiyar shirin a Janairu, bisa ga umarnin gwamnan.
Ekiti: Gwamna ya ba ma'aikata kyautar N42m
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji ya yaba da kokarin wasu ma’aikata 82 ta hanyar ba su kyautar tsabar kudi har N42m
A yayin wani taron kungiyar ma’aikatan gwamnati, Oyebanji ya yi wa ma’aikatan Ekiti alkawari kan inganta walwalarsu tare da ci gaba da biyan sabon albashi.
Gwamnan ya kuma yaba wa ma’aikatan bisa hakurin da suka nuna, ya yi alkawarin cewa nan ba da dadewa za su kara shan romon dimokuradiyya daga gwamnatinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


