Rigima za Ta Kare: Majalisar Dattawa Ta Bude Ofishin Natasha bayan Wata 6
- An bude ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya bayan watanni yana kulle a Majalisar Dattawa
- An rufe ofishin nata tun watan Maris na 2025 bayan da aka dakatar da ita daga ayyukan majalisar saboda rikicin shugabanci
- Hakan na zuwa ne bayan da wasu kungiyoyin mata sama da 350 sun kai korafi zauren majalisar dinkin duniya kan lamarin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Majalisar dattawa ta buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka rufe tun watan Maris 2025, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a siyasar Kogi da ma Najeriya baki ɗaya.
Ofishin nata, wanda yake ginin Majalisar Dattawa, an buɗe shi ne da safiyar Talata, 23 ga Satumban 2025.

Source: Twitter
Legit ta gano yadda aka bude ofishin ne a wani sako da tashar NTA ta wallafa a shafinta na X da safiyar yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin ya biyo bayan karewar wa’adin dakatar da Sanatar da aka ɗaura mata saboda zargin saba ka’idojin majalisa bayan wata takaddama da shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
An bude ofishin Sanata Natasha a Majalisa
Tun ranar 6 ga watan Maris 2025 aka kulle ofishin Natasha, lokacin da majalisar ta dakatar da ita har tsawon wata shida.
Dakatarwar ta fito ne daga zargin da ake yi mata na yin fito-na-fito da shugabancin majalisar yayin da aka sake mata kujerar zama.
A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga jami'in tsaro na majalisar, Alabi Adedeji, yana cire hatimi ja a ƙofar ofishin Sanatar tare da bayyana cewa an buɗe shi daga yau.
Wannan ya tabbatar da cewa matakin na hukuma ne daga bangaren tsaron majalisar dattawan Najeriya.
Kalubalen da Sanata Natasha ta fuskanta
A baya, kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci a ranar 4 ga watan Yuli cewa dakatar da Natasha tsawon wata shida ya wuce gona da iri.
Punch ta wallafa cewa kotun ta bayyana matakin a matsayin abin da bai dace ba da kuma saba wa kundin tsarin mulki.

Source: Facebook
Duk da karewar dakatarwar a watan Satumba 2025, ba ta samu damar komawa bakin aiki ba saboda rikicin shari’a da ke ci gaba.
Sanatar ta rubuta takarda zuwa majalisar domin sanar da niyyarta ta komawa bakin aiki, amma an ƙi karɓar bukatarta, abin da ya ƙara rura wutar rikicin siyasa.
Makomar Natasha a majalisar dattawa
A yanzu haka, babu tabbacin ko buɗe ofishin zai ba Natasha cikakken damar ci gaba da ayyukanta a zauren majalisar dattawa.
Shugabancin majalisar bai fitar da wata sanarwa ba kan matsayin Sanatar, kuma ana jiran ganin yadda za a yi lokacin da majalisar za ta sake zama a watan Oktoba.
Mata sun shigar da korafi saboda Natasha
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin mata sama da 350 sun kai karafi zauren majalisar dinkin duniya kan Sanata Natasha Akpoti.
Matan sun bukaci majalisar dinkin duniya ta matsawa gwamnatin Najeriya lamba wajen ganin an dawo da Sanatar bakin aiki.
Hakan na zuwa ne bayan rashin dawo da Natasha Akpoti ofis duk da cikar wa'adin wata shida na dakatar da ita da aka yi ya cika.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


