Al Sheikh: Limamin Arafa kuma Shugaban Malaman Saudiyya Ya Rasu
- Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da rasuwar Sheikh Abdulaziz Al Sheikh yana da shekara 82 a duniya
- Sarki Salman ya umarci gudanar da sallar jana’iza a Makka, Madina da sauran masallatai a faɗin Saudiyya
- Sheikh Al Sheikh ya jagoranci Majalisar Manyan Malamai kuma ya wallafa ayyuka da dama kan shari’a da fatawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Riyadh – Saudiyya ta sanar da rasuwar babban mufti na ƙasar, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah Al Sheikh, yana da shekara 82 a duniya.
Sarki Salman bin Abdulaziz ya bada umarni a gudanar da sallar jana’iza daga nesa a masallacin Harami na Makka, masallacin Annabi a Madina da sauran masallatai a faɗin ƙasar.

Source: Facebook
Legit ta samu rahoto kan rasuwar malamin ne a wani sako da shafin kasar Saudiyya na Inside the Haramain ya wallafa a X.
Haka kuma za a gudanar da jana’izar Sheikh Al Sheikh a yau a masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh bayan sallar la’asar.
Rayuwa da tarihin Sheikh Al Sheikh
Rahoton Gulf News ya nuna cewa an haifi Sheikh Abdulaziz Al Sheikh a Makka a ranar 30 ga Nuwamba, 1943.
Ya rasa mahaifinsa tun yana ƙarami, yana shekaru takwas, wanda hakan ya sa ya tashi a matsayin maraya.
Ya hardace Alƙur’ani mai girma tun yana ƙarami, daga baya kuma ya rasa gani a cikin shekarunsa na samartaka.

Source: AFP
Duk da haka, ya ci gaba da neman ilimin shari’a, inda ya zama ɗaya daga cikin fitattun malamai a jami’o’i da kuma majalisun ilimi.
Ya yi wa’azi a masallacin Imam Turki bin Abdullah na Riyadh tare da jagorantar hudubobi a masallacin Nimrah a lokacin aikin Hajji.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya shafe shekara 34 yana huduba a Arafa ga mahajjata daga 1982 zuwa 2015.

Kara karanta wannan
Zuwan Tinubu ya yi amfani, an kaddamar da ayyukan da za su taimaki musulmi a Sultan Bello
Matsayin da Al Sheikh ya rike a Saudi
Sheikh Al Sheikh ya rike mukaman da suka haɗa da babban mufti na Saudiyya, shugaban Majalisar Manyan Malamai, da kuma shugaban hukumar bincike da bayar da fatawa ta ƙasa.
Ya kasance babban marubuci a fagen shari’a, inda ya wallafa littattafai da dama kan akida, halal da haram, da kuma tattara fatawowi da ya bayar a lokuta daban-daban.
A matsayin babban mufti na uku a tarihin Saudiyya, ya gaji Sheikh Mohammed bin Ibrahim Al Shaikh da Sheikh Abdulaziz bin Baz.
Saudiyya ta yi wa duniya ta'aziyya
Sarki Salman da Yarima Mohammed bin Salman sun mika ta’aziyarsu ga iyalan marigayin, al’ummar Saudiyya da kuma musulmin duniya baki ɗaya.
Sun bayyana Sheikh Al Sheikh a matsayin ginshiƙi a fagen ilimin addini, mai bada gudummawa wajen tabbatar da koyarwar shari’a da kuma jagoranci ga musulmi.
Haka nan, kungoyoyi da dama a duniya sun bayyana ta'ziyya tare da nuna alhinin rashin babban malamin na addinin Islama.
Malamin musulunci ya rasu a Adamawa
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Modibbo Dahiru Aliyu Ganye ya rasu a Adamawa.
An bayyana cewa Sheikh Aliyu Ganye ya shafe shekaru yana karantar da mutane addinin Musulunci.
Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar malamin, inda ya roki Allah ya gafarta masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

