NiMet: Ruwan Sama Zai Sauka a Kano, Taraba, Nasarawa da Wasu Jihohi a Yau Talata
- Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama da iska mai karfi zai sauka a jihohin Najeriya a ranar 23 ga Satumba, 2025
- A safiyar Talatar, NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama mai yawa zai sauka a wasu jihohin Arewa kamar Kano, Tabara da Neja
- NiMet ta shawarci mazauna yankunan da ke yawan fuskantar ambaliyar ruwa da su dauki matakan kariya a wannan rana
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar da ke kula da yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na yau da kullum, wanda ta ce zai yi aiki a ranar Talata, 23 ga Satumba, 2025.
Hasashen NiMet ya nuna cewa za a samu ruwa da iska mai karfi a wasu jihohin Arewa da Kudancin Najeriya daga safiya zuwa daren Talata.

Source: UGC
NiMet ta fitar da wannan hasashen ne a cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X a daren ranar Litinin, 22 ga Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NiMet: Hasashen ruwan sama a Arewa
Da safiyar Talata, akwai yiwuwar samun ruwan sama mai sauki a sassan jihohin Kebbi, Taraba, da Adamawa, yayin da sauran yankuna za su kasance cikin yanayi na hadari.
Haka ma a Arewa ta Tsakiya, NiMet ta ce za a samu haduwar hadari da safe, amma rana za ta fito a mafi yawan jihohin shiyyar.
Akwai kuma yiwuwar hadari tare da saukar ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan jihohin Kogi, Nasarawa, Kwara, da Neja da kuma Babban Birnin Tarayya watau Abuja.
Ruwan sama da yamma a Arewa
Da yammaci zuwa dare kuma, NiMet ta ce za a samu ruwan sama da iska mai matsakaicin karfi a sassan jihohin Adamawa, Bauchi, Kaduna, Taraba, Gombe, Kano, Jigawa, da Borno.
NiMet ta kara da cewa, akwai yiwuwar za a fuskanci ruwan sama mai matsakaicin karfi a sassan jihohin Benuwai, Plateau, Kogi, Nasarawa, Kwara, da Neja.
Hasashen ruwan sama a jihohin Kudu
A yankin Kudancin Najeriya kuwa, NiMet ta yi hasashen samun yanayi na hadari tare da yiwuwar ruwan sama mai sauki a sassan jihohin Ebonyi, Abia, Imo, Oyo, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom, da Cross River da safiyar Talata.
Da yammaci zuwa dare kuma, an yi hasashen samun ruwan sama mai matsakaicin karfi a mafi yawan sassan jihohin Imo, Abia, Enugu, Anambra, Ebonyi, Ogun, Oyo, Ondo, Ekiti, Osun, Bayelsa, Edo, Delta, Rivers, Akwa Ibom, da Cross River.

Source: Original
Shawarwari da gargadi ga jama'a
Hukumar NiMet ta yi kira ga mazauna jihohin da aka ce za su samu ruwan saman da su yi taka tsantsan a yayin da suke gudanar da ayyukansu na waje.
An shawarci masu ababen hawa da su yi taka tsantsan a lokacin da suke tuki a ruwan sama saboda yadda ruwa mai karfi ke rage gani, wanda ka iya jawo hadurra.
Hukumar ta kuma kara da cewa, mazauna yankunan da suka saba fuskantar ambaliyar ruwa su dauki matakan kariya, domin ambaliyar na iya afkuwa.
Ambaliyar ruwa ta shiga gidaje 4,521 a Yobe
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mutane bakwai sun mutu, wasu 12,470 sun rasa muhallansu yayin da aka samu ambaliya a Yobe.
Ambaliyar ruwan ta afku ne a ranar 15 da 17 ga watan Agusta, 2025 a garuruwa daban daban na jihar, inda ta shafi gidaje 4,521, cewar hukumar SEMA.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Yobe ta bayyana cewa gwamnatin jihar na aiki tare da YOGIS da sauran hukumomi, don kai daukin gaggawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


