Mutuwa Ta Taba Manyan Sarakuna, Sarkin Ruman Katsina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mutuwa Ta Taba Manyan Sarakuna, Sarkin Ruman Katsina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Sarkin Ruman Katsina, Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu'azu ya rasu yana da shekaru 76 da haihuwa yau Litinin, 22 ga Satumba, 2025
  • Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya dade yana fama da rashin lafiya kafin ya koma ga Allah a gidansa da ke Batsari, jihar Katsina
  • Sanarwar ta iyalan mamacin suka fitar ta nuna cewa an yi jana'izar basaraken bayan sallar La'asar, da misalin karfe 4:30 na yammacin yau

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, ya riga mu gidan gaskiya.

Basaraken ya rasu ne a yau Litinin, 22 ga watan Satumba, 2025 bayan ya sha fama da jinya ta tsawon lokaci.

Marigayi Sarkin Ruman Katsina.
Hoton marigayi, Sarkin Ruman Katsina kuma hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu Hoto: Maaarautar Katsina a yau
Source: Facebook

Jaridar Aminiya, sashen Hausa na Daily Trust ta tattaro cewa Marigayin ya rasu yana da shekaru 76 a duniya.

Kara karanta wannan

Tsohon dan bindiga mai shekara 70 da ya ajiye makamai ya yi jawabi a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Ruman Katsina ya bar duniya

An tattaro cewa Alhaji Tukur Ma’azu ya shafe shekaru 43 yana rike da sarautar Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari kafin Allah ya karbi ransa a yau Litinin.

Sanarwa daga iyalan mamacin ta bayyana cewa an gudanar da jana’izar basaraken da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau a gidansa da ke cikin garin Batsari.

Marigayi Alhaji Tukur Ma’azu ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya da kuma jikoki da dama.

Gwamna Dikko Radda ya halarci jana'iza

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci sallar jana’izar marigayi Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma, tare da ɗaruruwan al’umma.

Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a Facebook.

An gudanar da sallar jana’izar a gidansa da ke Batsari, inda Babban Limamin Darika na garin, Imam Ishaq Suleiman, ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Kafa bataliya da wasu manyan alƙawura 4 da Tinubu ya yi wa Katsina kan ƴan bindiga

Gwamna Radda ya yiwa iyalan marigayin ta'aziyya a wannan lokaci mai raɗaɗi, sannan daga bisani ya raka gawar zuwa makabartar Batsari, wurin da aka birne shi.

Dikko Radda ya yi ta'aziyyar rasuwar hakimin

Bayan kammala jana’izar, Dikko ya bayyana marigayi Sarkin Ruman Katsina a matsayin gwarzon basarake wanda ya yi hidima ga al’ummarsa da jajircewa tare da barin gadon zaman lafiya da hidimar jama’a.

Gwamnan ya yi addu’ar samun rahamar Allah a gare shi, tare da roƙon Ubangiji Ya ba iyalansa haƙuri da ƙarfin juriya.

Wurin jana'izar Hakimin Batsari.
Hoton mutane a wurin jana'izar Sarkin Ruman Katsina a Batsari Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Ya ƙara tunatar da iyalan cewa su yi haƙuri da ƙaddarar Allah, domin rayuwa da mutuwa suna hannunSa ne.

"Allah Ya ji ƙan marigayi Sarkin Ruman Katsina, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma, Ya kuma ba shi wurin zama a Aljannatul Firdaus, Ya ba iyalansa ƙarfin zuciya don jure wannan rashi," in ji Gwamna Dikko.

Hakimin Kabo a Kano ya kwanta dama

A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Gabas kuma Hakimin Kabo, Alhaji Idris Muhammad Adamu DanKabo, ya bar duniya yana da shekaru 48.

Masarautar Kano ta tabbatar da wannan rashi, tana mai jimamin mutuwar marigayin Alhaji Idris wanda ya kasance mutum mai kan-kan da kai da mu'amala da al'umma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Daga bisani, masarautar ta yi addu'ar Ubangiji ya gafar ta masa ya kuma saka masa da gidan aljanna firdausi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262