Me Ke Faruwa? Mata 3 da Suka Ci Zaben Kansila, da Mataimakiyar Ciyaman Sun Mutu
- Ana ci gaba da tattaunawa game da wasu shugabannin siyasa mata hudu da suka mutu a cikin kasa da watanni biyu a Legas
- Oluwakemi Rufai, Zainab Shotayo, Princess Oluremi Ajose, da Basirat Mayabikan, sun mutu ne 'yan kwanaki bayan rantsar da su
- Yayin da mutane ke zargin matan ko sun hadu da sharrin 'yan siyasa ne, jam'iyyar APC ta fito fili ta magantu kan mutuwar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - An shiga jimami hade da damuwa a jihar Legas bayan mata hudu daga cikin zababbun shugabannin siyasa suka riga mu gidan gaskiya a cikin kasa da kwanaki 60.
Rahotanni sun bayyana cewa an rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi, mataimaka da kansiloli a ranar 27 ga Yuli, 2025 a Legas.

Source: Twitter
Bayanan zababbun mata 4 da suka mutu
Amma rahoton The Nation ya nuna cewa a cikin kwanaki 57 kacal bayan rantsuwar, mata hudu daga kananan hukumomi daban-daban sun mutu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin kansiloli uku da mataimakiyar shugaban karamar hukuma daya da suka mutu a Legas a kasa da watanni biyu:
1. Oluwakemi Rufai
Ta farko ita ce Oluwakemi Rufai, kansilar mazabar Ward C a karamar hukumar Ibeju-Lekki, wadda ta rasu a ranar 13 ga Agusta, kwanaki 17 bayan rantsuwa.
Mun rahoto cewa Oluwakemi Rufai ce kadai mace a majalisar karamar hukumar, inda aka ce ta mutu bayan gajeriyar rashin lafiya.
2. Zainab Shotayo
Kwana biyar bayan rasuwar Oluwakemi Rufai, a ranar 18 ga Agusta, Zainab Shotayo, kansilar mazabar Ward C3 a karamar hukumar Odiolowo-Ojuwoye, ta rasu.
Kamar Oluwakemi, ita ma Zainab, ita kadai ce mace a majalisar karamar hukumar kuma tana rike da mukamin bulalar majalisar ta shida kafin rasuwarta.
3. Princess Oluremi Nutayi Ajose
A ranar 20 ga Satumba, Princess Oluremi Nutayi Ajose, mataimakiyar shugaban karamar hukumar Badagry ta Yamma, ta rasu. Ta shafe kwanaki 55 kacal a kujerarta.

Kara karanta wannan
Ana sulhu da 'yan ta'adda a Katsina, 'yan bindiga sun sace hakimi da wasu mata 2 a Filato
Princess Oluremi Nutayi Ajose gimbiya ce, domin ta kasanec ’yar sarkin masarautar Apa Egun-Awori Kingdom, watau Oba Oyekan Possi Ajose, kamar yadda muka rahoto.
4. Basirat Oluwakemi Mayabikan
Mutuwa ta ake girgiza Legas yayin da Basirat Oluwakemi Mayabikan, kansilar mazabar Ward F a karamar hukumasr Shomolu, ta rasu a ranar 21 ga Satumba.
An rahoto cewa Basirat ta rasu ne kwanaki 56 bayan rantsuwarta da kama aiki, kuma ta kasance cikin majalisar karamar hukumar ta 10 kafin rasuwarta.
Rasuwar wadannan mata 'yan siyasa hudu cikin kasa da wata biyu ta tayar da hankula a jihar, inda rade-radi suka rika yawo, har wasu na zargin ko dai sun gamu da sharrin 'yan siyasa ne.

Source: Twitter
Mutuwar kansiloli: APC ta musanta jita-jita
Sai dai, jaridar Punch ta rahoto cewa jam’iyyar APC, reshen jihar Legas ta fito fili ta karyata hakan, tana mai cewa, babu sa hannun 'yan siyasa a mutuwar matan.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Seye Oladejo, ya bayyana jita-jitar da ake yadawa a matsayin marar tushe kuma rashin tausayi ga mamatan.
Seye Oladejo ya ce alakanta mutuwar matan da siyasa bai dace ba kuma rashin girmama iyalan mamatan ne.
Shugaban ya kara da cewa jam’iyyar APC ta dade tana ba mata muhimmanci a siyasa, tana kuma daukar matakai na musamman domin karuwar mata a mukaman gwamnati.
Mutuwar dai ta bar gibi a cikin majalisun kananan hukumomi tare da tunasar da jama’a cewa rayuwa a siyasa tana da matukar hadari.
Tsohon ciyaman da kansila sun mutu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, harin da ƴan bindiga suka kai kauyen Morai da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara ya yi ajalin mutane biyar.
Bayanan da ke kara fitowa daga majiyoyi masu karfi sun nuna tsohon kantoman Talata Mafara, Hon. Saminu Morai na cikin waɗanda aka kashe.
Bayan tsohon kantoma da aka kashe, an ce daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da tsohon kansila a karamar hukumar, Alhaji Akilu Liman.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

