'Kamar Abduljabbar,' Jalo Jalingo na Son Gwamna Radda Ya Hada Mukabala da Masussuka

'Kamar Abduljabbar,' Jalo Jalingo na Son Gwamna Radda Ya Hada Mukabala da Masussuka

  • Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya bukaci gwamnan Katsina ya shirya muƙabala tsakanin malamai da Yahaya Masussuka
  • Ya ce wannan mataki ya fi dacewa fiye da muƙabalar da aka shirya a Kano tsakanin malamai da Abduljabbar Kabara
  • A yanzu haka dai idanu sun karkata kan gwamnatin Katsina ko za ta amsa wannan kira domin shirya mukabalar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Shugaban malaman Izala na kasa, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya bukaci Gwamnan Jihar Katsina da ya shirya zaman muƙabala tsakanin malaman jihar da Yahaya Masussuka.

Dr Jalo Jalingo ya yi kiran ne bayan ya ce Masussuka na karyata dukkan hadisan Annabi Muhammadu (SAW).

Hotunan Dr Jalo, Masussuka da gwamna Radda
Hotunan Dr Jalo, Masussuka da gwamna Radda. Hoto: Ibrahim Jalo Jalingo|Masussuka TV|Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook, malamin ya ce muƙabala na da muhimmanci domin kare darajar Hadisai da kuma tabbatar da gaskiya a gaban al’umma.

Kara karanta wannan

Zaman sulhu: Sheikh Gumi ya gargadi jami'an tsaro kan 'yan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Jalo ya yi wannan kira ne da nuni da yadda tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya shirya irin wannan zama tsakanin malaman Kano da Abduljabbar Nasiru Kabara.

Dalilan neman mukabala da Masussuka

Dr Jalo ya bayyana cewa matsalar Yahaya Masussuka ta fi ta Abduljabbar Kabara muni, domin a cewarsa duk da Abduljabbar dan Shi’a ne, bai karyata dukkan hadisai gaba ɗaya ba.

Sai dai a cewar Dr Jalo, Abduljabbar Nasiru Kabara ya musanta wasu daga cikin hadisan da wasu daga cikin 'yan Shi’a ke musantawa.

Amma a cewar malamin, Masussuka ya ki yarda da kowanne hadisi face wanda ya kirkira da kansa.

A cewar shugaban malaman Izala, wannan hali na Masussuka ya sanya ya fi cancantar a titsiye shi ta hanyar muƙabala domin kare martabar sunnah da hadisan Annabi SAW.

Abduljabbar Nasiru Kabara da aka yi mukabala da shi a Kano a 2021
Abduljabbar Nasiru Kabara da aka yi mukabala da shi a Kano a 2021. Hoto: Sheikh Dr Abduljabbar Nasiru Kabara Fans
Source: UGC

Kiran Dr Jalo ga gwamnan Katsina

Dr Jalo ya yi kira kai tsaye ga Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda da ya dauki nauyin zama, tare da gayyatar manyan malaman jihar domin su yi muƙabala da Masussuka.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Abba Kabir ya kalubalanci mulkin Ganduje, ya yi masa gorin ayyuka

Ya ce hakan zai zama hujja a bainar jama’a kuma zai taimaka wajen kare akidar Musulunci daga barna.

Ya ce wannan mataki ne da ya dace da Gwamna Dikko Radda ya dauka domin kare mutuncin addini da kuma tabbatar da cewa batun karyata hadisai bai samu karbuwa a Katsina ba.

Martanin jama'a kan tayin mukabalar

Tun bayan kiran da aka yi, hankula sun koma kan gwamnatin Katsina don ganin ko za ta amince da shirin muƙabalar.

Wasu daga cikin masu sharhi kan maganar Dr Jalo sun bayyana cewa hakan zai kara tabbatar da gaskiya, yayin da wasu kuma ke ganin ya kamata a yi hattara da irin tattaunawar.

Dan agajin kungiyar Izala ya rasu a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban 'yan agajin Izala a jihar Katsina, Abdullahi Bakori ya rasu a makon da ya wuce.

Rahotanni sun bayyana cewa Bakori ya rasu ne a jihar Katsina kuma a nan aka masa jana'iza kamar yadda addini ya koyar.

Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki da ya taimaki addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng