Kafa Bataliya da Wasu Manyan Alƙawura 4 da Tinubu Ya Yi wa Katsina kan Ƴan Bindiga

Kafa Bataliya da Wasu Manyan Alƙawura 4 da Tinubu Ya Yi wa Katsina kan Ƴan Bindiga

  • Gwamna Dikko Radda ya yi magana bayan da ya jagoranci tawaga zuwa fadar shugaban ƙasa kan matsalar tsaro a jihar Katsina
  • A yayin ganawar, Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin samar da karin kayan yaƙi, da sansanonin tsaro a Kudancin Katsina
  • Gwamna Radda ya zayyano manyan alkawura biyar da Tinubu ya dauka, wadanda ake ganin za su dawo da zaman lafiya a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya daukar mata alkawura biyar domin ƙarfafa yaƙi da barayin daji.

Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan bayan ganawa da shugaban ƙasa a fadar Aso Rock, Abuja, inda ya jagoranci dattawa da malaman Katsina.

Dikko Radda ya bayyana alkawuran da Tinubu ya yi wa Katsina kan 'yan ta'adda
Shugaba Bola Tinubu yana musabaha da Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina. Hoto: @dikko_radda
Source: Facebook

Tawagar ta je neman taimakon gaggawa ne bayan harin da aka kai kan masallata a ƙaramar hukumar Malumfashi wanda ya girgiza jama’a, inji rahoton BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu zai zauna a mulki har ya mutu? Fadar shugaban kasa ta magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alƙawura 5 da Tinubu ya yi wa Katsina

A cewar Gwamna Radda, shugaban ƙasa ya bayyana wasu matakai biyar da zai ɗauka domin magance matsalar tsaro a Katsina.

Na farko, Tinubu ya ce zai umurci jami’an tsaro su sauya dabarun da suke amfani da su wajen yaƙi da ’yan ta’adda.

Na biyu, ya yi alkawarin samar da karin ƙarfin sama, musamman tura jirage marasa matuƙa da za su iya kai hare-hare da jefa bama-bamai.

Na uku, shugaban ƙasa zai rika tattaunawa da shugabannin tsaro akai-akai domin ya karɓi rahoton abin da ke gudana a fagen yaƙi da 'yan ta'adda.

Na huɗu, ya tabbatar da cewa za a kafa bataliya ta musamman a Kudancin Katsina domin ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin.

Na biyar, akwai yarjejeniya da rundunar ’yan sanda cewa za a buɗe sababbin sansanonin sintiri a Kudancin jihar.

Sauyin da aka gani a yaki da 'yan ta'adda

Kara karanta wannan

2027: Gangar siyasa ta fara kaɗawa, Sanata ya ƙaddamar da kungiyar zaɓen Tinubu

Gwamna Radda ya kara da cewa kafin waɗannan sababbin alkawura, jihar ta riga ta samu karin jami’an tsaro wanda ya rage yawan hare-hare.

Ya ce haɗin gwiwar sojoji, ’yan sanda, jami’an tsaro na jihar da maharba daga Maiduguri ya taimaka wajen fatattakar barayin daji.

A cewarsa:

“Yanzu hare-haren sun ragu. Wani lokaci ma sai ka ga an daina kai hari a wasu wurare kwata-kwata.”
Dikko Radda ya ce Tinubu ya yi alkawarin samar da karin tsaro da jirgen yaki ga jihar Katsina.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda a gidan gwamnati Hoto: @dikko_radda
Source: Facebook

Sulhu da 'yan bindiga a jihar Katsina

Dikko Radda ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta biya ’yan ta’adda kuɗi don su daina kai hare-hare ba, amma idan al’umma suka nemi sulhu, za su yi maraba da hakan.

Ya bayyana cewa a wasu ƙananan hukumomi kamar Batsari, Jibiya, Danmusa da Safana, an samu sassaucin hare-hare sakamakon sulhu da 'yan bindiga.

Sai dai a wasu yankunan da ba a samu sulhu ba, barayin dajin suna ci gaba da kai hare-hare, abin da ya sa gwamnati ta matsa ƙaimi wajen yakarsa.

Katsina: Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dakarun sojoji na Operation FANSAN YANMA a jihar Katsina suka fatattaki ’yan ta’adda a wani kwanton bauna.

Kara karanta wannan

Katsina: Kananan hukumomi 2 sun zauna da ƴan ta'adda ɗauke da mugayen makamai

Lamarin dai ya faru ne lokacin da dakarun ke sintiri a hanyar Kankara–FUDMA–Makera–Dutsinma–Dabawa, inda aka kai musu hari a kauyen Turare.

Hakazalika, an yi musayar wuta mai zafi tsakanin sojoji da 'yan ta'adda a Faskari da Kankara, inda sojoji suka kwato babura guda bakwai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com