Katsina: Kananan Hukumomi 2 Sun Zauna da Ƴan Ta'adda Ɗauke da Mugayen Makamai
- An gudanar da tarukan zaman lafiya tsakanin shugabannin ‘yan bindiga da wasu yankuna a jihar Katsina
- Rahotanni sun bayyana cewa an yi zaman ne da kananan hukumomi biyu na Katsina da ke fuskantar hare-hare
- Ƴan ta'addan da suka halarci zaman dauke da mugayen makamai sun yi alkawarin dakatar da kashe jama'a
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina – An kuma gudanar da taron zaman zaman lafiya tsakanin shugabannin ‘yan bindiga da kananan hukumomi biyu a Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa wakilai a ƙananan hukumomin Sabuwa da Matazu na jihar Katsina ne su ka wakilci jama'arsu a zaman.

Source: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa a Sabuwa, taron ya gudana a kauyen Dugun Muazu, domin kawo zaman lafiya a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zauna da ƴan ta'adda a Katsina
The Cable ta ta ruwaito cewa wadanda suka halarci taron sun haɗa da Sagir Tanimu, shugaban karamar hukuma, da Ibrahim Danjuma, ɗan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar yankin.
Haka zalika, Umar Manmada, mai ba gwamna shawara kan asibitoci, da Ibrahim Ibrahim (Yarima Kogo), dattijo a yankin, sun kasance a wajen taron.
A gefe guda kuma, manyan shugabannin ‘yan bindiga da suka halarci taron sun haɗa da Kabiru, Maisaje, Kachalla da Adamu Risku.

Source: Twitter
Sai kuma Idi Mawange, Kachalla Damina, Kachalla Murtala, Kachalla Shua’ibu, Kachalla Dawa da Kachalla Maitantan.
Rahoton ya ce batutuwan da suka fi daukar hankali a tattaunawar sun shafi sasantawa da kuma dakatar da kai hare-hare.
Ɓangarorin biyu sun yi alkawarin jajircewa wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Katsina: An gana da ƴan ta'adda a Matazu
A rana ɗaya guda, an gudanar da irin wannan taro a ƙaramar hukumar Matazu, a makarantar firamare ta Yargeza da ke Dan-Musa.
Shamsuddeen Sayaya, shugaban karamar hukuma, tare da Iro Maikano, hakimin yankin, ne suka jagoranci zaman zaman lafiya.
A ɓangaren ‘yan bindiga kuwa, waɗanda suka shiga taron sun haɗa da Muhammadu, Sani Yellow da Ummaru Manore, ta hannun mai shiga tsakani, Hamisu Bastari.
Taron ya ɗauki kusan awa ɗaya da mintuna 40, inda aka kammala shi da misalin 3.40 na rana.
Daga bisani, ɓangarorin biyu sun yi alkawarin yin aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Matazu da kewaye.
Katsina: Ɗan bindiga ya fara cika alkawari
A baya, mun wallafa cewa jagoran ‘yan bindiga, Isiya Akwashi Garwa, ya fara aiwatar da yarjejeniyar sulhu ta hanyar sakin mutanen da yake garkuwa da su.
Ya fara sakin mutanen ne a karamar hukumar Faskarin jihar Katsina bayan an yi zaman sulhu da wasu shugabannin 'yan bindiga da su ka hana zama lafiya a yankin.
An saki mutane 28 ba tare da an biya kudin fansa ba, daga kauyuka da su ka hada da Mairuwa, Kanon-haki da Yar Dabaru domin cika wani ɓangare na yarjejeniyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

