Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Kasurgumin Jagoran 'Yan Bindiga a Zamfara
- Rundunar ’yan sanda ta kama jagoran ’yan bindiga Muhammadu Kan Kani (Akki), daga ƙaramar hukumar Bungudu, Zamfara
- An samu nasarar cafke hatsabibin dan bindigar ne a hanyar Kano zuwa Yankara (Katsina) bayan samun sahihan bayanan sirri
- Muhammadu Kan Kani ya amsa cewa yana jagorantar ’yan bindigar da ke addabar Tsafe, Yandoto da Yanwaren Daji a Zamfara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Rundunar ’yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da kama wani fitaccen jagoran ’yan bindiga da aka fi sani da Muhammadu Kan Kani.
'Yan sanda sun cafke Kan Kani, wanda aka fi sani da Akki, mai shekara 57 daga kauyen Kuraje, ƙaramar hukumar Bungudu da Zamfara.

Source: Twitter
An cafke hatsabibin dan bindiga a Zamfara
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa an kama Kan Kani ne a ranar 17 ga Satumba, 2025 bayan samun sahihan bayanan sirri.
Majiyoyin sun bayyana cewa jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane, tare da haɗin gwiwar takwarorinsu a jihar Katsina, ne suka cafke shi a lokacin da yake tafiya daga Kano zuwa Yankara da ke Katsina.
A cewar majiyar, wanda ake zargin ya amsa cewa yana jagorantar ’yan bindigar da suka addabi garuruwan Tsafe, Yandoto da Yanwaren Daji.
Ya kuma bayyana wa 'yan sanda cewa yana ɗaya daga cikin ’yan tawagar Kachalla Dan Goggo, wadda take addabar Damba, Mareri da Saminaka a ƙaramar hukumar Gusau.
Majiyoyi sun ce ana ci gaba da bincike a kansa, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.
An kama wasu 'yan kungiyar IPOB/ESN
A lokaci guda, rundunar ’yan sanda ta tabbatar da kama wasu mutum biyar da ake zargi da kasancewa mambobin haramtacciyar ƙungiyar IPOB da reshen ta na tsaro, ESN.
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola cewa an kama su ne a jihohin Imo da Rivers yayin wasu samame da aka kai bisa dogara kan bayanan leƙen asiri.
An bayyana sunayen da aka kama da suka haɗa da: Iwuji Chima (33), Chimezie Uwala (32), Kingsley Melete (51), Chinemere Nwoke (24), da Ogochukwu Nwoke (30), wadda ita ce matar wani kwamandan ESN mai suna Charles da ake nema yanzu haka.

Source: Twitter
Yadda aka kama 'yan IPOB a Rivers
Majiyoyin sun ce an cafke su ne bayan wani dogon aikin bin sawu da ya fara daga garin Elele a Rivers da misalin ƙarfe 1:15 na safe a ranar 20 ga Satumba.
An rahoto cewa, jami'an tsaro sun ci gaba da bin sahun wadanda ake zargin har zuwa Agwa, da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo da misalin ƙarfe 4:50 na safe.
An ce waɗanda aka kama sun amsa laifin aikata ayyukan ta’addanci da nufin ganin an kafa ƙasar da suke kira Jamhuriyar Biafra.
Majiyoyi sun ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere.
An cafke mai sayarwa Turji makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami'an tsaro a jihar Sokoto, sun kama Hamza Suruddubu, mai samar da makamai ga Bello Turji.
Suruddubu yana safarar makamai daga Zamfara zuwa Gabashin Sokoto, yana sayarwa manyan 'yan ta’adda, ciki har da Halilu Buzu.
Wata majiya ta yi zargin cewa akwai sa hannun jami'an tsaro a safarar makaman da ake yi a yankunan Isa da Sabon Birni, Sokoto.
Asali: Legit.ng


