Kwankwaso, Dangote da Manyan Mutane Sun Je Auren 'Yar Gidan Dantata a Kano
- Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci daurin aure tsakanin Faisal Mohammed Bello Adoke da Amira Sayyu Dantata a Kano
- Rahotanni sun nuna cewa bikin ya gudana ne a Masallacin marigayi Alhaji Alhassan Dantata da ke unguwar Koki, jihar Kano
- Fitattun mutane tsakanin 'yan kasuwa da 'yan siyasa ciki har da Sanata Ibrahim Dankwambo sun samu halartar a wajen bikin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kasance cikin manyan bakin da suka halarci daurin auren iyalan Dantata a Kano.
An daura auren ne tsakanin ɗan tsohon ministan shari’a na tarayya, Faisal Mohammed Bello Adoke da Amira Sayyu Dantata, ‘yar attajiri Sayyu Idris Dantata.

Source: Facebook
Hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Saifullahi Hassan ne ya wallafa yadda aka gudanar da auren a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Tinubu, 'yan siyasa, malaman Izala da Darika sun cika Kaduna auren dan Sanata Yari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An daura auren 'yar Sayyu Dantata
An gudanar da daurin auren ne ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025, a Masallacin Alhaji Alhassan Dantata da ke unguwar Koki, cikin jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa jama’a daga fannoni daban-daban sun hallara domin shaida muhimmiyar ranar.
Kwankwaso ya yi addu’a da fatan Allah Ya albarkaci auren da zaman lafiya da dawwamammen farin ciki.
Aliko Dangote ya halarci daurin auren
Bikin ya ja hankalin manyan baki daga sassa daban-daban na kasa, ciki har da sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda aka hangi kasancewarsa a wajen.
Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo da ke wakiltar Gombe ta Arewa tsohon Akanta Janar ne na tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Gombe.
Haka zalika attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote na cikin wadanda suka shaida daurin auren a yau Asabar.
Malamai da dattijai sun gabatar da addu’o’i na fatan alheri ga ma’auratan, tare da jaddada muhimmancin gina iyali bisa tsari da tarbiyya.

Source: Facebook
Su wane ne Sayyu Dantata da Adoke?
Sayyu Idris Dantata, mahaifin Amira, ya shahara a Najeriya da ma ƙasashen duniya saboda nasarorin da ya cimma a harkokin kasuwanci.
Rahoton The Sun ya nuna cewa shi ne wanda ya kafa MRS, kamfani mai fannonin zuba jari a makamashi, masana’antu, harkar jigila, gidaje da kuma noma.
Sayyu Idris ya fito daga sanannen gidan Dantata mai dogon tarihi, kuma ɗan uwa ne ga attajirin Afirka, Aliko Dangote.
Mahaifin angon, Muhammad Bello Adoke masanin doka ne kuma ya rike mukamin Ministan shari'a a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.
Bayan zuwan shugaba Muhammadu Buhari, an budo wasu takardun bincike da suka shafi rashawa da suka jawo bincike game da Muhammad Bello Adoke.

Source: Twitter
A watan Yulin da ya gabata ne Adoke ya kaddamar da wani littafi a Abuja, inda ya yi bayani game da zargin da aka masa a baya.
A daura auren 'dan Kwankwaso a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa an daura auren dan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da auren Mustapha Rabiu Kwankwaso ne ba tare da fitar da gayyata ga jama'ar duniya ba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya kasance wakilin Mustapha yayin da malamai kamar Sheikh Aminu Daurawa suka shaida daurin auren.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

