Tashin Hankali: Bam Ya Tarwatse da Yara 'Yan Firamare Suna Wasa cikin Aji a Benue
- Dalibai bakwai sun gamu da mummunan rauni a makarantar firamare a jihar Benue, bayan wani abu da ake zargi bam ne ya tashi
- An rahoto cewa, daliban sun tarar da bam din a cikin aji, inda suka dauka suna wasa da shi cikin rashin sani, har ya tarwatse da su
- Yayin da aka saki sunayen yaran da abin ya rutsa da su da kuma halin da suke ciki, 'yan sanda sun fara neman IED a makarantar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Akalla dalibai bakwai suka jikkata, yayin da wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya tashi da su a ranar 16 ga watan Satumba, 2025.
An ce abin fashewar (IED) ya tarwatse da yaran ne a makarantar firamare ta LEA, Ater Ayange a karamar hukumar Ukum, jihar Benue.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An samu gawar shugaban hukumar NDLEA a wani irin yanayi a dakin otal

Source: Getty Images
Bam ya tashi da 'yan firamare a Benue
Jaridar The Cable ta rahoto cewa fashewar ta auku ne misalin karfe 2:00 na rana, lokacin da yaran suka tarar da wani abu a cikin makaranta, suka fara wasa da shi ba tare da sanin cewa bam ba ne.
Bayan fashewar bam din, an ce an garzaya da yaran zuwa asibitin St. Anthony’s da ke Zaki-Biam, inda ake kula da su kuma aka ce suna samun sauƙi.
Likitoci da ma’aikatan jinya sun tabbatar da cewa dukkan yaran suna samun kulawar da ta kamata, kuma babu wanda aka ce ya rasa ransa a harin.
Rundunar ‘yan sanda ta dauki mataki
Rahoton ya nuna cewa lamarin bai je ofishin ‘yan sanda ba sai ranar 18 ga Satumba, lokacin da DPO na Ukum ya samu bayanai, kuma ya tura jami’ai zuwa makarantar da kuma asibitin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue, Udeme Edet, ya tabbatar da cewa sashen lalata bama-bamai (EOD) ya ziyarci makarantar domin binciko ko akwai wasu sauran bama-bamai da aka ɓoye. Haka kuma, sashen CID ya fara bincike kan lamarin.
“’Yan sanda suna kan bincike. An tura tawagar EOD zuwa karamar hukumar Ukum domin tantance ko akwai wasu bama-bamai da aka bari a wurin."
- Udeme Edet.

Source: Original
Sunayen 'yan firamare da suka jikkata
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar SUBEB a jihar Benue, Ioryue Thomas, ya fitar da krin rahoto kan lamarin a wani dandalin SUBEB na Facebook.
A cewar bayanan Ioryue Thomas, daliban da abin ya rutsa da su sun hada da:
- Abigail Terseer (Aji biyar)
- William Msaaga (Aji shida)
- Tyolumun Deborah (Aji shida)
- Terseer Mhenuter (Aji uku)
- Mzungwega Mnengeuter (Aji biyu)
- Aondohemba Luper (Aji daya)
- Ba a bayyana sunan dalibi na bakwai ba
Ya ce yaran sun tarar da abin fashewar ne a cikin aji, kuma suka fara wasa da shi, daga nan sai ya tarwatse da su, lamarin da ya sa suka jikkata.
Kalli hotunan yaran a nan kasa:
Bam ya tarwatse da yara suna wasa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani abin fashewa ya tarwatse da wasu yara uku a jihar Borno a lokacin da su ke tsaka da wasa a yankin Pulka.

Kara karanta wannan
Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan
An rahoto cewa yaran sun taka abin fashewar da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka dasa shi a yankin, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsu gaba daya.
Bayan an garzaya da su asibiti ne, likitoci su ka tabbatar da cewa yaran uku, wadanda dukkansu mata ne - Fati Dahiru, Aisha Ibrahim, da Fati Yakubu - sun rasu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
