Kiristoci Sun Yi Magana kan Dokar Haramta Wa'azin Addini a Niger, Sun Fadi Matsayarsu

Kiristoci Sun Yi Magana kan Dokar Haramta Wa'azin Addini a Niger, Sun Fadi Matsayarsu

  • Kungiyar matasan Kirista ta tura sako musamman ga gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago kan dokar wa'azi
  • Kungiyar ta yi watsi da dokar wa’azi ta gwamnatin tana kiran matakin da tilastawa, wariya da cin zarafin ’yancin addini ne
  • Gwamna Umar Bago ya kare dokar, yana mai cewa ba ta hana wa’azi ba, illa dai ta magance kalaman da ka iya ta da rikici

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Ana ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabambanta game dokar haramta wa'azi ba tare da lasisi ba a jihar Niger.

Malamai da kungiyoyin Kiristoci da na Musulunci sun bayyana matsayarsu kan dokar a jihar.

Kiristoci sun yi martani kan dokar wa'azi a Niger
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Niger. Hoto: Gov. Mohammaed Umaru Bago.
Source: Twitter

Niger: Kirisotci sun soki haramta wa'azi

Wata kungiyar matasan Kiristoci ta yi watsi da sabuwar dokar wa’azi da gwamnatin Jihar Niger ta kawo, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dattawan Arewa sun fusata bayan ikirarin APC kan takarar 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta yi fatali da dokar tana cewa kwata-kwata ba ta dace ba, tana nuna wariya, kuma zalunci ce.

Majiyoyi sun nuna cewa dokar ta tilasta masu wa’azi a jihar su gabatar da hudubarsu kafin a amince su gabatar a bainar jama’a.

Sai dai kungiyar, ta bakin Paul Adama, ta bayyana cewa wannan mataki tozarci ne ga ’yanci, kuma ya sabawa kundin tsarin mulki.

"Jihar Niger ta yi suna a kwanan nan saboda dalilai marasa kyau, baya ga matsalar tsaro, gwamnati ta kara jawowa jama’a matsala da wannan doka."

- Cewar sanarwar

An taso Gwamna Bago a gaba kan doakr haramta wa'azi
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago. Hoto: Gov. Mohammed Umaru Bago.
Source: Facebook

Dalilin sukar dokar da kungiyar ta yi

Kungiyar ta ce dokar nuna tsangwama ce da take ’yancin dan Adam, ta yi nuni da Sashe na 38 da 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya, Daily Post ta ruwaito.

Har ila yau, ta ce addini abu ne mai matukar sosa rai a Najeriya, don haka gwamnati ta kula wajen daukar mataki da zai iya ta da hankali.

Kara karanta wannan

2027: APC, PDP sun fara nuna wa juna yatsa kan karya dokar INEC

Ta roƙi gwamnatin Niger ta janye dokar domin zaman lafiya, adalci, da mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya da ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar ta ce:

"Mun tsaya kan kyakkyawar fahimtar addini, muna kin duk wata magana da ka iya ta da rikici.
"Mun roki gwamnati ta soke dokar nan da ta wajabta lasisi da gabatar da huduba domin tantancewa da amincewa."

Baya ga batun addini, kungiyar ta jawo hankalin gwamnati kan matsalolin da suka fi tasiri ga al’umma irin su tsaro da yawaitar talauci.

"Tattaunawa kan talauci, tsaro, rashin ingantaccen ababen more rayuwa da koma baya su ne abubuwan da ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali."

- Kungiyar matasan Kiristoci

Gwamna Bago ya zauna da yan bola jari

Kun ji cewa Gwamna Mohammed Umaru Bago ya ce gwamnati ba za ta amince da masu fakewa da bola jari su ci gaba da satar kayayyaki ba.

A karkashin haka, gwamnan Niger ya bukaci shugabannin ƙungiyar su tantance mambobinsu tare da gano masu laifi a cikinsu.

Gwamnatin ta shirya babban taro tare da hukumomin tsaro da shugabannin ƙungiyar na kananan hukumomi 25 na jihar Niger don neman mafita.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.