SRRBDA: Darakta Ya Ci Kudin Haram a Katsina, An Daure Shi a Gidan Yari kan N305,000

SRRBDA: Darakta Ya Ci Kudin Haram a Katsina, An Daure Shi a Gidan Yari kan N305,000

  • Babbar Kotun Katsina ta yanke wa darakta a hukumar SRRBDA, Rabiu Musa Matazu hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari
  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, 2025
  • Kotun ta kama Rabiu Matazu da laifin karbar kudi N305,000 a madadin hukumar kula da ruwan Rima amma ya karkatar da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Kotun Jihar Katsina ta yanke wa jami’in Hukumar Kula da Ruwan Rima na Sakkwato (SRRBDA) hukuncin shekaru biyar a gidan yari bisa laifin karkatar da kudin haya N305,000

Babbar kotun wacce ke zamanta Jihar Katsina ta yanke wannan hukunci ne a karar da hukumar yaki da rashawa (ICPC) ta shigar gabanta.

Kara karanta wannan

NECO ta saki sakamakon jarabawa, an gano makarantu 38 a jihohi 13 sun yi magudi

Hukumar ICPC.
Hoton babban ofishin hukumar ICPC da ke Abuja Hoto: @ICPCNigeria
Source: Facebook

Rahoton jaridar Vanguard ya tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar ICPC ta fitar jiya Laraba, 17 ga watan Satumba, 2025.

Wane laifi daraktan SRRBDA ya aikata?

ICPC ta ce babbar kotun jihar Katsina ta samu Rabiu Musa Matazu, Daraktan Sashen Gudanarwa na hukumar SRRBDA, da laifi a kan tuhume-tuhume hudu da aka shigar kansa.

Tuhume-tuhumen dai sun shafi amfani da mukaminsa wajen karkatar da dukiyar kaaa da kuma cin amana.

Lauyoyin ICPC sun shaida wa kotu cewa Rabiu Matazu ya karɓi N305,000 da sunan hukumar, sannan ya karkatar da kudaden zuwa aljihunsa.

Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta laifin tun da farko, lamarin da ya jawo dadewa ana fafata shari'ar.

Tuhume-tuhumen da ICPC ta shigar a kotu

A takardar tuhume-tuhumen, ICPC ta shaida wa kotu cewa:

“Kai Rabiu Musa Matazu, a watan Oktoba 2014, ka yi amfani da matsayinka na Daraktan Gudanarwa don amfanar da kanka ta hanyar karɓar kuɗin haya N305,000 da aka tattara a madadin SRRBDA, ka karkatar zuwa aljihunka.”

Kara karanta wannan

NECO ta fadi lokacin sakin sakamakon jarrabawar dalibai na shekarar 2025

Bayan shafe shekaru uku ana gwabza shari’a, Mai shari’a Abbas Bawule ya same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhumen.

Kotu.
Hoton gudumar da alkali ke amfani da ita a kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hukuncin da kotu ta yanke

Kotun ta yanke masa hukuncin watanni shida a gidan yari ko kuma biyan tarar N20,000 a kan tuhuma uku, sannan shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin tara ba a kan tuhuma ta hudu.

ICPC ta bayyana cewa wannan hukunci wani ɓangare ne na ƙoƙarin dakile cin hanci da rashawa a Najeriya, ƙasar da ta dade tana fama da wannan matsala.

Hukumar ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da bakin kokarinta wajen ganin ta kawar da duk wani nau'in cin hanci a fadin kasar nan, in ji rahoton Premium Times.

Kotu ta amince ICPC ta binciki jami'an Kano

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya Mai Zama a Abuja ta tabbatar da cewa ICPC na da cikakken ikon bincikar batun almundahanar kuɗin tallafin karatu a Kano.

Tun farko dai wasu jami’an gwamnatin Kano sun nemi a hana Hukumar ICPC gudanar da bincike kan zargin almundahanar kuɗin tallafin karatun.

Kara karanta wannan

'Dabarar da aka yi Katsina ta kawo karshen 'yan bindiga da kashi 70,' Gwamnati

Sai dai kotun ta yi fatali da karar, inda ta bayyana cewa hukumar ICPC na da hurumin gudanar da bincike kan badakalar da ake zargi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262