Asiri Ya Tonu: An Kama Gidan da ake Kera Bindigogi a Filato, an Gano Makamai
- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kai samame a masana’antar haramtattun makamai a Heipang, Barkin Ladi, Filato
- An cafke wani ƙwararren mai ƙera makamai tare da kwato bindigogi da dama da sauran harsasai daban-daban a wajensa
- Rundunar soji ta ce za ta ci gaba da kawar da makamai a yankin don tabbatar da tsaro a Arewa ta Tsakiya da kasa baki daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Plateau – Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan wata masana’antar haramtattun makamai a unguwar Heipang, ƙaramar hukumar Barkin Ladi a jihar Plateau.
Wannan aikin ya biyo bayan sahihan bayanan leƙen asiri da aka samu kan ayyukan wata ƙungiya da ke kera makamai a yankin.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu bayanai kan yadda aka gano wajen kera makaman ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan
Dangote ya ce ana neman ya saka tallafin man fetur na Naira tiriliyan 1.5 a Najeriya
A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya fitar, an samu nasarar kama wani daga cikin masu kera makaman yayin da wasu suka tsere kafin isowarsu.
Samame na daga cikin jerin matakan da rundunar ke ɗauka domin kawar da haramtattun makamai da kuma tabbatar da tsaro a fadin jihar Plateau da sauran sassan Arewa ta Tsakiya.
An gano bindiga 13 a Filato
Binciken da aka gudanar a cikin masana’antar ya haifar da gano makamai masu yawa da aka ƙera da hannu.
Cikin makaman da aka gano akwai bindigogi iri daban-daban guda 12 da wata bindiga kirar pistol guda daya.
Haka kuma an samu tarin harsasai na bindigogi kala daban daban a wajen mutumin yayin bincike a gidan.
Baya ga haka, sojojin sun kuma kwato gurnati, radiyo, wuka mai kaifi, da kuma wani bokiti cike da magunguna daban-daban.

Source: Facebook
Matakin da sojoji suka dauka
Manjo Zhakom ya bayyana cewa an tsare wanda aka kama tare da kayan da aka kwato domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakin doka.
Ya ƙara da cewa rundunar tana ci gaba da bin diddigin sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere, tare da ƙoƙarin dakile ayyukansu gaba ɗaya.
Ya jaddada cewa sojoji ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen dakile yada makamai da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Alkawarin rundunar soji ga jama’a
Rundunar sojin Najeriya ta yi alkawarin ci gaba da kai irin waɗannan wurare domin hana 'yan ta'adda samun damar amfani da makamai wajen cutar da al’umma.
An bayyana cewa tsaron jama’a da dorewar zaman lafiya na ɗaya daga cikin muhimman manufofin ayyukan hadin gwiwar sojoji a Arewa ta Tsakiya.
'Yan bindiga sun kafa sharudan sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da tattaunawa kan batun sulhu da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin bukatun da 'yan ta'addan suka gabatar akwai gina musu makarantu.
Masana sun bayyana cewa za a iya yarda da wasu daga cikin bukatunsu amma da sharadin yin taka tsantsan da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

