Rivers: Ƴan Majalisa Sun Dauki Matakin Farko bayan Tinubu Ya Janye Dokar Ta Baci
- Majalisar dokokin jihar Rivers ta fara zama bayan bayan Shugaba Bola Tinubu ya janye dokar ta-baci a jihar mai arzikin mai
- Rikicin siyasa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara, Nyesom Wike da majalisa ya haifar da sanya dokar ta-baci a watan Maris
- Tinubu ya ce sulhu da haɗin kai tsakanin manyan masu ruwa da tsaki ya buɗe kofa ga dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Rivers
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rivers – 'Yan majalisar dokokin jihar Rivers sun dawo da zamansu na majalisa da ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.
Dawo da zaman majalisar na zuwa ne 'yan awanni kaɗan bayan sanarwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye dokar ta-baci a jihar.

Source: Twitter
'Yan majalisar Rivers sun fara zama
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa majalisar, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisa, Hon. Martin Amaewhule, za ta fara zama a rukunin gidajen majalisar da ke kan hanyar Aba–Port Harcourt.
Rahotanni sun nuna cewa mambobin majalisar guda 27 sun isa jihar kwanaki kafin karewar dokar ta-baci, kuma yanzu haka sun shirya fara zamansu na farko.
Ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, an ce 'yan majalisa, masu zama a rukunin gidajen majalisar sun riga da sun fara haduwa don fara zaman.
Dalilin kakaba dokar ta-baci a Rivers
A watan Maris din 2025 ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Rivers bayan ya bayyana cewa rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da majalisar dokoki ya jawo “durƙushewar mulki gaba ɗaya.”
Tinubu ya ce rikicin ya taɓa manyan kadarorin tattalin arzikin jihar, musamman bututun mai da ake lalatawa, abin da ya sanya dole ya dakatar da gwamnati da majalisar dokoki na tsawon watanni shida.
A lokacin, ya nada tsohon shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (rtd), a matsayin shugaban rikon ƙwarya domin tafiyar da jihar mai arzikin mai.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

Source: Facebook
Rikicin siyasa tsakanin Fubara da Wike
Fubara wanda ya gaji Nyesom Wike, ya shiga rikici da magabacinsa kasa da shekaru biyu a ofis, kan ikon sarrafa jam’iyyar PDP da tsarin siyasa a jihar.
Wannan rikici ya ratsa har majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule, abin da ya tilasta wa Tinubu yin katsalandan bisa tanadin Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki na 1999.
A sabon jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya ce bincike ya nuna cewa an samu sabuwar fahimta a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a Rivers domin komawa tafarkin dimokuraɗiyya cikin gaggawa.
Shugaban ƙasar ya gode wa sarakunan gargajiya da al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka bayar daga lokacin da aka kafa dokar har zuwa ƙarewarta.
APC na so Fubara ya koma jam'iyyarta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, APC ta sake gabatar wa gwamnan Ribas jihar, Siminalayi Fubara tayin komawa cikin jam'iyyarta.
Wannan na zuwa ne lokacin da aka fara shirye-shiryen dawo da Fubara kan mulki bayan watanni shida na dokar ta baci ya cika.
Mai magana da yawun APC reshen jihar Ribas, Darlington Nwauju, ya ce kamata ya yi Fubara ya shiga APC kafin ranar dawo da shi kan mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

