NAHCON Ta Nuna Damuwa, Sheikh Pakistan Ya Hango Matsalar da Za a Iya Samu a Hajjin 2026

NAHCON Ta Nuna Damuwa, Sheikh Pakistan Ya Hango Matsalar da Za a Iya Samu a Hajjin 2026

  • Shugaban NAHCON na kasa, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya gana da gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda
  • Babban malamin ya ce ya gana da Dikko ne domin neman goyon bayansa wajen jawo hankalin maniyyata su biya kudin Hajji da wuri
  • Sheikh Pakistan ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya ba alhazai a 2024 ya taimaka wajen samun nasara a aikin Hajjin shekarar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta nuna damuwa kan jinkirin biyan kuɗaɗen aikin Hajjin 2026 daga maniyyatan da ke shirin sauke farali a badi.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman (Pakistan), ne ya nuna wannan damuwa yayin da yake hira da ‘yan jarida a ranar Laraba, bayan ganawa da Gwamna Dikko Radda.

Shugaban NAHCON da Gwamna Dikko Radda.
Hoton shugaban NAHCON da tawagarsa lokacin da suka ziyarci Gwamna Dikko Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Dalilin NAHCON na zuwa wurin Dikko Radda

Kara karanta wannan

Amupitan: Jam'iyyar ADC ta aika sako ga sabon shugaban INEC da Tinubu ya nada

A ruwayar Daily Trust, ya ce jinkirin biyan kuɗin kujerun Hajji na iya jawo matsalar rasa samun wuraren kwana masu kyau ga mahajjata a biranen Makka da Madina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Abdullahi Pakistan ya ce ya ziyarci Gwamna Radda ne domin neman goyon bayansa a matsayin shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma, wajen jawo hankalin maniyyata su biya kudin Hajji da wuri

Ya kuma bayyana tallafin shugaban ƙasa a aikin Hajjin 2024 a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da hukumar ta samu a ƙarƙashin Bola Tinubu.

Shugaban hukumar NAHCON ya yabawa Bola Tinubu

“Duba da matsin tattalin arzikin da ake ciki, musamman saboda sauya tsarin musaya, shugaban kasa ya ba da tallafin Naira biliyan 90 a aikin Hajjin 2024, domin saukaka wa mahajjatanmu.
“Haka kuma, ya amince da bayar da Naira biliyan 24 don biyan bashi da kamfanonin jiragen sama suke bi a Hajjin 2023, wanda hakan ya cece su daga fuskantar durƙushewa.
“Bugu da ƙari, gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da masu jigilar mahajjata domin su karɓi kuɗin gida, wanda hakan zai kare mahajjata daga matsalolin canjin kudi."

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

- Farfesa Abdullahi Saleh Usman.

Shugaban NAHCON na kasa, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan.
Hoton shugaban hukumar NAHCON ta kasa, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan Hoto: @Nahcon
Source: Twitter

Hajji: NAHCON ta fadada asusun gata

Shugaban NAHCON ya ƙara da cewa, wani muhimmin mataki da aka ɗauka shi ne dakatar da tsarin amfani da katin kuɗi wajen biyan kuɗaɗen tafiya daga mahajjata.

Ya ce manufar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gabatar ba za ta amfanar da mahajjatan Najeriya ba, saboda rashin wadataccen wayar da kai, in ji rahoton Guardian.

Abdullahi Pakistan ya ce:

“Gwamnatin tarayya ta kuma faɗaɗa tsarin asusun gata don tara kudin Hajji ta hanyar samar da karin bankuna, hakan zai bai wa maniyyata damar ajiye kuɗi a hankali a hankali na tsawon lokaci."

NAHCON ta fitar da kudin kujerar Hajjin 2026

A wani labarin, kun ji cewa NAHCON ta gudanar da taron tattaunawa kan aikin Hajjin 2026 tare da shugabanni da sakatarorin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohin Najeriya.

A jaawabinsa a wurin taron, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya nuna godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da yake baiwa alhazai.

Kara karanta wannan

Amupitan: Farfesa daga jami'ar Jos na dab da zama sabon shugaban hukumar INEC

Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, shugaban NAHCON ya ce an amince maniyyata su fara ajiye ₦8.5m domin aikin Hajjin 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262