NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawa, An Gano Makarantu 38 a Jihohi 13 Sun Yi Magudi
- Hukumar NECO ta ce ta fara bincike kan wasu makarantu 38 da ake zargi da zamba a lokacin jarabawar SSCE na 2025
- Shugaban NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi, ya ce za a gayyaci makarantun zuwa hukumar kafin a hukunta su yadda ya dace
- Farfesa Wushishi ya kuma fadi matakin da NECO ta dauka game da wasu daliban Adamawa da rikici ya sa ba su yi jarabawa ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Hukumar shirya jarabawar NECO, ta fara bincike kan makarantu 38 da aka kama da laifin yin magudi a jarabawar SSCE ta 2025.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da shugaban hukumar, Farfesa Ibrahim Wushishi, ya fitar a Minna, jihar Neja, yayin fitar da sakamakon jarabawar na bana.

Source: Facebook
NECO: Za a binciki makarantu 38
Jaridar Punch ta rahoto Farfesa Wushishi ya ce za a gayyaci makarantun da aka kama da wannan laifi daga jihohi 13.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar shugaban NECO, hukumar za ta gudanar da tattaunawa da makarantun 38 kafin daukar matakan ladabtarwa da suka dace.
Farfesa Wushishi ya bayyana cewa, duk da rage yawan laifuffukan magudin jarabawa a bana idan aka kwatanta da bara — daga 10,094 a 2024 zuwa 3,878 a 2025 — akwai babbar matsala da ta shafi makarantun da suka shiga cikin wannan laifi.
Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ta ce daga cikin dalibai 1,367,210 da suka yi rajista (maza 685,514, mata 681,696), jimillar dalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.
2025: NECO ta sallami jami'anta 9
Shugaban hukumar ya kara da cewa hukumar ta sallami jami’ai tara da ke aiki da ita a wuraren da ake gudanar da jarabawa, inji rahoton The Nation.
Wadanda aka sallama sun haɗa da masu lura da dalibai uku daga Rivers, ɗaya daga Neja, uku daga Abuja, ɗaya daga Kano, da ɗaya daga Osun.
Laifuffukan da suka aikata sun hada da sakaci, taimakawa wajen magudi, yin jinkiri wajen daukar matakai, rashin ladabi, haddasa tashin hankali, da rashin bin ka’idar hukumar.

Source: Twitter
An samu tashin hankali a Adamawa
Hukumar ta kuma yi nuni da wani tashin hankali da aka samu a karamar hukumar Lamorde, Jihar Adamawa, inda rikicin al’umma ya katse jarabawar dalibai daga ranar 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.
"Game da abin da ya faru a karamar hukumar Lamorde, jihar Adamawa, makarantu takwas ne abin ya shafa, inda ba su iya zana jarabawar darussa 13 ba, haka kuma, an rasa damar yin zama 29 na jarabawar."
- Farfesa Ibrahim Wushishi.
Hukumar ta ce tana tattaunawa da gwamnatin jihar domin sake gudanar da jarabawar ga daliban da abin ya shafa.
'Akwai bukatar wayar da kan dalibai' - Sanusi Mani
A zantawarmu da Sanusi Ya'u Mani, wakilin daliban hakimin Mani da ke jihar Katsina, ya ce akwai bukatar makarantu, shugabannin al'umma da kungiyoyin dalibai su fara wayar da kan dalibai kan zana jarawabar NECO, WAEC da komfuta.
Sanusi Ya'u Mani na magana ne game da sauya tsarin zana jarabawar kammala sakandare da gwamnatin tarayya ta yi daga takarda zuwa kwamfuta, wanda zai fara daga 2026.
"Sakamako ne mai kyau, duk da cewa yayi kasa, amma za mu iya cewa sakamakon ya yi kyau tun da kashi sama da 60 sun samu kiredit 5.
"Duk da hakan, na tabbatar, idan makarantu suka zage damtse wajen koyar da yara, sannan su ma iyaye suka dage wajen tabbatar da yaran suna karatu, to yaran za su mayar da hankali sosai, wanda zai sa su rika cin jarabawar.
"Abin da nake son jawo hankalinmu a kai shi ne wannan sabon tsarin jarabawar da za a kawo daga 2026, watau, zana jarabawa ta hanyar kwamfuta.
"Lallai yana da muhimmanci mu tashi tsaye, tun daga kan makarantu, shugabannin al'umma, kungiyoyin ilimi da sauransu, a koyar da yaranmu yadda za su sarrafa kwamfuta."
- Sanusi Ya'u Mani.
Wakilin daliban hakimin Mani ya nuna cewa ana samu yawaitar faduwar JAMB saboda mafi akasari yara basu iya kwamfuta ba, don haka, wasu har lokaci ya cika, ba su rubuta komai ba, ba kuma don ba su iya ba.
Ya kara da cewa:
"Mu dauki darasi da JAMB da UTME, za mu ga cewa ana samun matsala ne daga dalibai ta fuskar rashin iya sarrafa kwamfuta. Wani ko 'mouse' bai iya rikewa ba, wani ko shafin gaba ba zai iya budewa ba. Har lokaci ya cika ba su iya gane kan abun ba."
NECO za ta fitar da sakamakon jarabawa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, NECO ta bayyana cewa za ta saki sakamakon jarrabawar SSCE ta 2025 a ranar Laraba, 17 ga Satumba a jihar Neja.
Shugaban hukumar, Farfesa Ibrahim Wushishi, ne zai jagoranci fitar da sakamakon a shelkwatar NECO da ke Minna.
Haka kuma, hukumar za ta gudanar da bikin karrama ma’aikatanta da suka yi ritaya da domin jinjina masu a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



