Shugaban NECO ya bayyana jihohin da ake mumunar satar Amsar jarabawa, Kano, Bauchi ke kan gaba
- Jihar Kano, Bauchi da Bauchi sun fito zakaru cikin jihohin da ake mugun magudin jarabawa
- Daliban sakandare na zana jarabawar NECO kowace shekara don kammala karatunsu
- Shugaban NECO ya gabatar da jawabi kan yadda za'a magance matsalar satan jarabawa
Abuja - An bayyana jihar Bauchi, Kano da Kebbi a matsayin jihohin da ake mumunar magudin jarabawar kammala karatun Sakandare a Najeriya.
Shugaban hukumar Jarabawar kasa, NECO, Dantani Wushishi, ya bayyana haka, rahoton Punch.
Wushishi ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron shugabannin makarantun dakehada karatun Boko da na Islamiyya mai take, 'Illar magudin zabe: Magance matsalar don cigaban kasa.'.
Ya kara da cewa magudi da satar amsa a jarabawa sun yi muni a Arewacin Najeriya amma abin ya fi muni a jihohin Bauchi, Borno, Kano da Kebbi a shekaru 5 da suka gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Wushishi,
"A 2016, alkaluman magudin jarabawa sun nuna Bauchi na 8.17%, Kaduna 6.20%, Kano 5.51%, Plateau 5.31%, da Sokoto 8.87%.
"A 2017, Bauchi (10.79%), Kebbi (16.06%), Borno (7.87%) da Kano (7.29%)."
"A 2018, Kano (12.45%), Kebbi (10.71%), Gombe (5.40%) da Zamfara (5.14%)."
"A 2019, Bornu (13.08%), Kano (11.70%), Kebbi (8.67%), Taraba (5.04%) and Yobe (6.56%)"
"Hakazalika a 2020, Adamawa (18.51%), Bauchi (7.88%), Kaduna (6.87%), Kano (7.88%) da Katsina (18.01%)."
Wushishi ya ce a shekaru biyar da suka gabata, Bauchi, Borno, Kano da Kebbi akafi samin satar jarabawa a Najeriya.
Nasarawa Poly ta sallami dalibai 51 kan laifin satar amsa a Jarabawa
A wani labarin, hukumar makarantar fasaha ta jihar Nasarawa watau Naspoly ta fittitiki dalibar 51 kan laifin satar amsa a jarabawar da aka gudanar a kakar karatun 2019/2020.
Mai magana da yawun makarantar, Uba Maina, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba, rahoton NAN.
Mana yace kwamitin ingancin ilimi na makarantar ta amince da a sallami daliban.
Ya lissafa daliban tsangaya-tsangaya da aka sallama, daga cikinsu har da dalibai aikin jarida.
Asali: Legit.ng