NiMet: Za a Samu Ruwa da Iska Mai Karfi a Abuja da Jihohin Arewa Ranar Alhamis
- Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta yi hasashen hadari da ruwan sama a mafi yawan sassan Najeriya a ranar Alhamis
- An yi hasashen cewa ruwan sama tare da iska mai karfi za su sauka a sassan Taraba, Kano, Bnenue da wasu jihohin Arewa takwas
- Hukumar ta shawarci mazauna yankunan da su fuskanci ambaliyar ruwa da su dauki matakan kariya tun kafin zuwan ambaliyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta kasa (NiMet), ta fitar da sabon hasashen yanayi na ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.
Hukumar NiMet ta yi gargadin cewa za a samu ruwan sama hade da iska mai karfi da kuma tsawa a Abuja da jihohi da dama na ƙasar.

Source: UGC
Hasashen ruwan safiya a Arewa
Hasashen da NiMet ta fitar a shafinta na X a ranar Laraba, ya nuna cewa akwai yiyuwar tsaiko a harkokin sufuri da sauran ayyuka saboda ruwan sama da iska mai ƙarfi.
A cewar NiMet, za a tashi da yanayi na hadari a safiyar Alhamis a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Sai dai kuma akwai yiyuwar ruwan sama mai matsakaicin karfi da zai sauka a jihar Taraba.
A Arewa ta Tsakiya kuwa, za a samu haduwar hadari da iska mai karfi, sannan ruwan sama ya biyo baya a Abuja da jihohin Kogi, Benue, Kwara da Niger.
Hasashen ruwan saman yamma a Arewa
Da yammacin ranar ta Alhamis, jihohi da dama ciki har da Kaduna, Kebbi, Kano, Katsina, Zamfara, Adamawa da Taraba za su fuskanci ruwan sama da iska mai karfi.
Wannan na iya haifar da tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa da ayyukan noma a wasu sassan yankin, a cewar rahoton NiMet.
NiMet ta ce mafi yawan jihohin Arewa ta Tsakiya za su iya ci gaba da fuskantar ruwan sama mai yawa.
Wannan na iya kawo cikas ga tafiye-tafiye da kuma aikin gwamnati da na kasuwanci a babban birnin tarayya da kewaye.
Hasashen ruwan sama a yankin Kudu
A kudancin ƙasar kuwa, jihohi irin su Ekiti, Ebonyi, Anambra, Enugu, Akwa Ibom da Cross River za su samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a safiyar Alhamis.
Amma daga yamma, ana hasashen ruwan sama da iska mai karfi zai sauka a yawancin jihohin Kudancin kasar nan.
Wannan na iya shafar zirga-zirgar ababen hawa, harkokin kasuwanci da kuma lafiyar jama’a, musamman a yankunan da ake yawan samun ambaliya.

Source: UGC
Shawarwari daga hukumar NiMet
Hukumar ta gargadi manoma da su guji amfani da takin zamani ko magungunan feshi kafin ruwan sama ya sauka domin kada a yi asarar amfanin gona.
Haka kuma ta shawarci direbobi da su yi tuƙi cikin natsuwa saboda ruwa sa iska za su iya rage hangen nesa, sannan titi zai yi santsi, wadanda za su iya jawo hadurra.
Bugu da ƙari, an yi kira ga mazauna wuraren da ke fama da ambaliya su ɗauki matakan kariya, yayin da aka umarci hukumomin ba da agajin gaggawa da su kasance cikin shiri su ma.
Ambaliya ta yi barna a jihar Kebbi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki masu yawa a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ambaliyar ruwan dai ta shafi wasu kauyuka ne a kananan hukumomin Dandi da Suru na jihar Kebbi bayan da aka samu saukar mamakon ruwan sama.
Gwamnatin jihar ta kai ziyarar jaje inda ta ba tallafin kudi da abinci ga mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa tare da daukar matakan kariya don gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


