Shugaba Tinubu Ya Fadi Dalilin Janye Dokar Ta Baci a Rivers

Shugaba Tinubu Ya Fadi Dalilin Janye Dokar Ta Baci a Rivers

  • Shugaban kasa Tinubu ya kawo karshen watanni shida na dokar ta-baci da ya ayyana a jihar Rivers
  • Hakan na nufin Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da 'yan majalisa za su koma aiki daga 18 ga watan Satumba, 2025
  • Mai girma shugaban kasan ya yi tsokaci kan dalilin da ya sanya ya ayyana dokar ta-bacin tun da farko

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye dokar ta bacin da ya sanya a jihar Rivers.

Shugaba Tinubu ya umarci jwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa kan su koma bakin aiki daga gobe.

Shugaba Tinubu ya janye dokar ta baci a Rivers
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara Hoto: @SimFubaraKSC, @DOlusegun
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya rattabawa hannu, wadda mai magana da yawun bakinsa, Bayo Onanuga, ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

A karshe, Shugaba Tinubu ya cire dokar ta bacin da ya sanya a jihar Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 18 ga watan Maris 2025, bayan wani taro da shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci na tsawon watanni shida a jihar Rivers.

Meyasa Tinubu ya janye dokar ta-baci?

A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya ce ya samu kwarin gwiwa daga sababbin al’amura da suka nuna alamar sulhu da shirin shugabannin jihar Rivers na komawa tafiyar da mulki ta hanyar dimokuraɗiyya.

"Akwai sabon yanayi na fahimtar juna, da cikakken shiri, da kuma kwazo daga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa a jihar Rivers don komawa mulkin dimokuraɗiyya ba tare da bata lokaci ba."
"Saboda haka ban ga dalilin da zai sa dokar ta-baci ta ci gaba da wanzuwa fiye da watanni shida da na ayyana a farko ba."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya yi kira ga gwamnoni da ‘yan majalisa a fadin kasar nan da su tuna cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne ginshikai na kawo wa ‘yan Najeriya amfanin dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Tinubu, Fubara sun dawo Najeriya ana shirin dawo da gwamnan Ribas kujerarsa

Tinubu ya magantu kan sa dokar ta-baci

Yayin da yake tuna dalilan da suka sa aka ayyana dokar ta-baci, Tinubu ya bayyana cewa harkokin mulki a jihar Rivers sun tsaya cak saboda rashin jituwa tsakanin gwamna da 'yan majalisar dokoki.

Ya nuna cewa majalisar dokokin jihar ta kasu gida biyu, inda mambobi hudu kawai ke goyon bayan gwamna, yayin da 27 suka tsaya tare da kakakin majalisa, lamarin da ya hana gabatar da kasafin kuɗi da kuma gudanar da ayyukan gwamnati.

Shugaba Tinubu ya janye dokar ta bacin da ya sanya a Rivers
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Tinubu: Dokar ta-baci ta ceto jihar Rivers

Shugaban kasan ya bayyana cewa duk da cewa sama da ƙarar kotu 40 aka shigar don kalubalantar matakin, hakan wani ɓangare ne na tsarin dimokuraɗiyya.

Amma ya jaddada cewa dokar ta-bacin ta zama tilas domin dawo da zaman lafiya, saboda jihar ta kusa shiga rudani gaba ɗaya.

Shugaban APC ya yabi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta tanka bayan Atiku ya yi suka kan matsalar yunwa da talahci

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa manufofin da shugaban kasan yake aiwatarwa, sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Shugaban na APC ya bayyana cewa a sakamakon manufofin, jihohi sun koma suna iya biyan albashi ba tare da tangarda ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng