ICPC: Kotu Ta Jika wa Gwamnatin Kano Aiki kan Tsarin Tallafin Karatu
- Kotu ta tabbatar da cewa ICPC na da cikakken ikon bincikar batun almundahanar kuɗin tallafin karatu a Kano
- Wannan na zuwa ne bayan lauyoyin hukumar ilimi da hukumar tallafin karatu ƙalubalanci hukumar kan kokarin bincikenta
- Jami'an gwamnatin Kano sun kai ƙara kotu, inda su ke bayyana cewa ICPC tana yunkurin ta ke hakkin dan adam da sunan bincike
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin mai shari’a Josephine Obanor, ta yi watsi da koken gwamnatin Kano bayan an fara yunkurin bincikenta.
Wasu jami’an gwamnatin Kano sun nemi a hana Hukumar ICPC gudanar da bincike kan zargin almundahanar kuɗin tallafin karatu a jihar.

Source: Facebook
A saƙon da ICPC ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce kotu ta tabbatar da cewa tana da hurumin gudanar da binciken.
ICPC ta fara bincike a Kano
Hukumar ta ce ta fara binciken tsarin tallafin karatun saboda wani ƙorafi da aka shigar wa hukumar gabanta a kwanakin baya.
Ta ce ƙorafin na zargin ana amfani da kuɗin tallafin karatu ba bisa ƙa’ida ba, wanda hakan ya tauye hakkokin dalibai.
A yayin bincike, hukumar ta ICPC ta gayyaci jami’an ma’aikatar ilimi ta Kano da hukumar tallafin karatu domin gabatar da hujjoji da takardu kan zargin.
Sai dai wadanda aka gayyata domin bayar da bayanin na su bayyana a gaban hukumar ba kamar yadda aka nema.
Jami'an gwamnatin Kano sun tafi kotu
Sai dai maimakon su amsa gayyatar, jami’an da Dr. Hadi Bala, babban sakataren ma’aikatar ilimi sun garzaya kotu.
Sun shigar da ƙara mai lamba CV/2857/2025 kan babban lauyan gwamnati da ICPC, suna zargin cewa an tauye musu haƙƙinsu.

Source: Facebook
A hukuncin da ta yanke, mai shari’a Obanor ta ce wasiƙar gayyata daga ICPC ba za ta iya zama tauye haƙƙin ɗan adam ba, domin kawai gayyata ce ta bincike.
Saboda haka kotun ta ce ba a nuna kowanne irin take hakki ba, ta kuma tabbatar da cewa ICPC na da ikon gudanar da bincike bisa doka.
Wannan ya sa ta yi watsi da ƙarar bisa rashin cancanta da tabbatar da ikon ICPC ta ci gaba da bincikenta da ta ke yunkurin fara wa bayan karbar korafin wasu bayin Allah.
ICPC ta dura kan kakakin majalisar Kano
A baya, kun samu labarin cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) ta aike da takardun gayyata ga kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore.
Haka kuma an aika takarda ga mataimakinsa Muhammad Butu, da wasu mutane uku domin amsa tambayoyi kan zargin badakalar kwangilar magunguna da ta kai Naira miliyan 440.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mataki wani bangare ne na binciken da ICPC ke gudanarwa kan yadda kudin kwangilar magungunan ya bace ko kuma aka karkatar da shi.
Asali: Legit.ng

