Malami Ya Shiga Rikici da Gwamna, Ana Zarginsa da Ingiza Ta'addanci a Jihar Kebbi
- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya ce tsohon ministan shari’a Abubakar Malami na amfani da siyasa wajen yada ayyukan ta’addanci
- Idris ya karyata zargin Malami cewa gwamnatin Kebbi ta shigo da ‘yan bangan siyasa, ya ce hakan barazana ce ga zaman lafiya
- Tuni kusoshin APC a majalisar tarayya da wasu kungiyoyi sun bukaci hukumomi su sanya Malami a jerin masu tallafawa ta’addanci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Birnin Kebbi – Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya zargi tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), da daukar siyasa a matsayin wata hanya ta yada “ayyukan ta’addanci.”
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin yayin da yake karɓar bakuncin tawagar kungiyoyin fararen hula da suka kai masa ziyarar goyon baya.

Source: Facebook
Zargin da Malami ya yi wa gwamnati
Malami, wanda jigo ne a jam’iyyar adawa ta ADC, ya rubuta takardar koke ga manyan hafsoshin tsaro, ciki har da NSA da CDS, inda ya yi ikirarin cewa gwamnatin Kebbi ta shigo da ‘yan bangar siyasa don razana 'yan adawa, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takardar tasa, wacce aka rubuta ranar 10 ga Satumba, ta biyo bayan hari da aka kai wa ayarin motocinsa, inda aka lalata wasu daga cikin motocin.
"Abin takaici ne, yadda wasu 'yan bangar siyasa daga hedikwatar APC ta jihar, dauke da makamai, suka farmaki ayarinmu, suka lalace ababen hawa da raunata magoya bayanmu."
- Abubakar Malami.
Sai dai tun a lokacin, APC ta fito ta nesanta kanta daga wannan hari da aka kai wa ayarin motocin Abubakar Malami.
Gwamna Idris ya caccaki ministan Buhari
Amma Gwamna Idris ya karyata zargin, yana mai cewa kalaman Malami sun riga sun fara tsoratar da masu zuba jari daga kasashen waje da ke shirin kafa masana’antu a Kebbi.
Jaridar Punch ta rahoto ya ce wasu masu kwangilar manyan tituna ma sun bar wuraren aiki saboda tsoron karuwar matsalar tsaro, wanda kalaman Malami suka haddasa.
Gwamna Idris ya ce:

Kara karanta wannan
Malami ya debo ruwan dafa kansa, 'yan Majalisa sun nemi jami'an tsaro su kama shi
“Wannan zargi nasa ba komai ba ne illa makirci na siyasa da nufin tada hankalin jama'a. Wannan ya yi kama da yunƙurin hana cigaban tattalin arzikinmu."
Gwamnan ya kuma karyata zargin Malami na cewa gwamnati ta shigo da 'yan daba, alhalin a cewarsa:
"Yan dabar da shi Malami ya yo hayarsu daga jihohin makwabta ne suka kai hari Birnin Kebbi a makon da ya gabata."

Source: Facebook
Martanin 'yan majalisa da kungiyoyin siyasa
Zargin ya sa kusoshin APC a majalisar tarayya, karkashin jagorancin Sanata Muhammad Aliero, suka bukaci a kama Malami tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
Kungiyar Coalition for Justice and Equity ma ta bukaci a saka Malami cikin jerin masu tallafawa ta’addanci, tana mai cewa abinda ya yi “makirci ne don tada rikici.”
Haka zalika, shugabannin APC a Kebbi sun nuna cikakken goyon bayansu ga Idris, inda suka amince da shi don yin tazarce, suna zargin Malami da “yunƙurin tayar da fitina.”
Gwamnati ta fito da barnar Malami a Kebbi
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kebbi ta barranta kanta da harin da tsohon Abubakar Malami ya ce an kaiwa ayarinsa.

Kara karanta wannan
Ganduje ya kafa kwamiti, zai binciki gwamnatin Kano kan korar kwamandojin Hisbah 44
Mashawarci na musamman ga gwamnan Kebbi kan yada labarai, Yahaya Sarki ya bayyana cewa mutanen Malami ne su ka fara neman husuma.
Ya jaddada cewa suna da hujjoji da shaidun da ke tabbatar da cewa ba 'yan APC ne su ka takali Malami ba, hasali ma kare kansu su ka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
