'Yan Bindiga Za Su Kashe Tsohon Dan Majalisa, Sun ba Gwamnati Wa'adin Kwanaki 4
- Gwamnatin jihar Imo ta yi alkawarin yin duk abin da ya dace don ganin ta ceto Ngozi Ogbu, tsohon ɗan majisa da aka sace
- A ranar 7 ga Satumba, 2025 ne wasu da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne, ɗauke da makamai suka sace Mista Ngozi
- Wadanda suka sace tsohon dan majalisar, sun ce za su kashe shi idan gwamnati ba ta biya bukatunsu a kwanaki hudu ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Imo - Gwamnatin jihar Imo ta lashi takobin yin duk mai yiwu wa don ceto tsohon ɗan majalisar dokokin jihar, Ngozi Ogbu, da aka sace.
Wannan na zuwa ne yayin da masu garkuwa da mutane da suka sace Ngozi Ogbu, suka yi barazanar kashe tsohon dan majalisar.

Source: Twitter
An yi barazanar kashe tsohon dan majalisa

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji
A baya, The Punch ta ruwaito cewa wasu mutane ɗauke da makamai, waɗanda suka yi iƙirarin cewa su 'yan kungiyar Biyafara ne, sun sace Mista Ogbu a karamar hukumar Onuimo ta jihar Imo a ranar 7 ga Satumba.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa an ga ɗaya daga cikin ‘yan ta’addan da suka sace tsohon ɗan majalisar a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu, yana jawabi.
'Dan bindigar ya yi ikirarin cewa shi mamba ne na ƙungiyar sojoji ta Biyafara da ke karkashin wata ƙungiya mai suna Autopilot IPOB, ƙungiyar ƴan aware da ake zargin Simon Ekpa ya kafa.
Ya kuma sha alwashin cewa za su kashe Ngozi Ogbu idan gwamnati da mutanen gari suka gaza janye jami'an tsaron da aka ce an tura wani wuri da ake kira White House a Okigwe, cikin wa'adin kwanaki hudu, da zai kare yau Talata.
'Yan sandan jihar Imo dai sun ce tuni aka tura jami'an tsaro daga sashen yaki da 'yan ta'adda domin ceto tsohon dan majalisar.
Gwamnati ta yi martani ga 'yan bindiga
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da Premium Times ta gani a ranar Lahadi, kwamishinan yaɗa labarai na Imo, Declan Emelumba, ya ce gwamnatin jihar tana yin duk abin da za ta iya don tabbatar da an sako Mista Ogbu.
Mista Emelumba ya ce gwamnatin ta yi Allah wadai da wannan aika-aika da kuma rashin bin doka da ya kai ga sace Mista Ogbu da ƴan ta’addan suka yi.
Ya ƙara da cewa:
"Tare da hukumomin tsaro, gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka wajaba don tabbatar da ceto shi cikin gaggawa, kuma a koshin lafiya."

Source: Original
Gwamnati ta gargadi 'yan siyasa
Kwamishinan ya yi gargadi ga ‘yan siyasa da su daina amfani da halin da Mista Ngozi Ogbu yake ciki wajen neman wani tagomashi na siyasa.
“Tsoma siyasa a cikin wannnan hali da yake ciki, ba karamin masifa ba ne, domin ko ba komai, abin ya shafi rayuwar uba, kuma ɗan’uwan mu, a taƙaice, abu ne mai girman gaske.”
- Declan Emelumba.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar Imo ta nanata jajircewarta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi a jihar.
'Yan bindiga sun sace tsohon dan majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan ta'adda dauke da miyagun makamai sun sace Festus Edughele, tsohon dan a majalisar dokokin jihar Edo.
An tattaro cewa tsohon dan majalisar na hanyar zuwa garin Benin, babban birnin jihar daga Orhionmwon don hawa jirgin sama lokacin da aka sace shi.
Tsohon mai magana da yawun majalisar dokokin jihar, Festus Ebea ya tabbatar da faruwar al’amarin, tare da yin karin bayani kan lamarin.
Asali: Legit.ng

