Naira Ta Rike Wuta, Darajarta Ta Karu yayin da Asusun Kudin Wajen Najeriya ke Habaka
- Darajar Naira na ci gaba da armashi bayan darajarta ta kai ₦1,500/$1 a kasuwar musayar kudin kasar nan, har ya haura haka a bayan fage
- Rahotanni sun ce Naira ta dawo da karfinta saboda sababbin tsare-tsaren kudi da Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso ya kawo
- Masana sun bayyana wasu daga cikin dalilan da Naira ke kara daraja, da kuma yadda gwamnati ta ta tabbatar hakan ya dore
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Darajar Naira na ci gaba da armashi bayan darajarta ta kai ₦1,500/$1 a kasuwar musayar kudin kasar nan, wato Nigerian Foreign Exchange Market.
Rahotanni sun bayyana cewa Naira ta dawo da karfinta saboda sababbin tsare-tsaren kudi da Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso ya bijiro da su.

Source: Getty Images
Daily Trust ta wallafa cewa yanzu haka, ajiyar asusun ajiyar Najeriya na kasashen waje ya kai $41.66bn a ranar 11 ga Satumba 2025.
Najeriya ta yi watanni 47 ba ta tara wadannan kudi a asusunta ba sannan kuma ana rahoto cewa kaya suna cigaba da yin sauki a yau.
Darajar Naira na karuwa
Rahoton ya ci gaba da cewa masana tattalin arziki suna ganin cewa waɗannan sauye‑sauyen da aka aiwatar a karkashin Olayemi Cardoso duna haifar da da mai ido.
A kasuwar musayar kudin, an canji Naira tsakanin ₦1,498 da ₦1,507 a makon da ya gabata, yayin da a kasuwar bayan fage kuma, ta kai tsakanin ₦1,515 zuwa ₦1,517 a kan kowace Dala.
Rahoton ya ce karuwar buƙatar Naira daga ‘yan kasuwa da kamfanoni, musamman waɗanda suke bukatar kudin kasar nan domin harkokinsu ya taimaka matuka.
Ana fatan Naira ta rike darajarta
Masana kan harkokin kudi na kamfanin Commercio Partners sun ce karfin da Naira ta samu kwanan nan ya samo asali ne daga samuwar abubuwa da dama.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dauki harama, nan ba da jimawa ba za a daina dauke wuta a Najeriya

Source: UGC
Sun alakanta hakan da karuwar buƙatar amfani da Naira, ƙaruwar ajiyar kudin a asusun gwamnati na kasashen waje da sauransu.
Shugaban sashen bincike a Commercio Partners, Ifeanyi Ubah, ya bayar da tabbacin cewa Naira za ta ci gaba da samun darajarta ake ganin ta samu a yanzu.
Ya ce:
“Ajiyar kudin waje na Najeriya ya kai $41.66bn a ranar 11 ga Satumba, 2025, kuma ya ci gaba da haɓaka cikin ‘yan makonni, abin da ke nuni da cewa halin tattalin arzikin wajen ƙasa ya ƙara ƙarfi."
Sai dai wasu masana sun yi gargadi cewa dorewar wannan ci gaban da Naira ta samu zai danganta ne ga yadda gwamnati za ta ci gaba da daidaita tattalin arziki,
Sai kuma bunƙasa hanyoyin samun kudin shiga daga kayayyakin da ba na mai ba domin a kara samun kudi a asusun gwamnati.
An kama masu wulakanta Naira
A baya, kun ji cewa Wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, Legas, ta yanke hukuncin daurin watanni shida ga fitattun ’yan TikTok biyu, TDollar da TobiNation kan wulakanta Naira.

Kara karanta wannan
Najeriya ta tattaro harajin sama da N600bn daga Facebook da wasu kamfanonin intanet
Hukuncin ya biyo bayan gurfanar da su da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi a gaban kotu, inda suka amsa laifinsu ba tare da sun baiwa kotu wahala ba.
Wadanda aka kama da laifin sun gurfana a gaban alkalin kotun, Alexander Owoeye, inda aka tuhume su da karya dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta hanyar watsa Naira a wajen biki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
