Fadar Shugaban Kasa Ta Tanka bayan Atiku Ya Yi Suka kan Yunwa da Talauci
- Fadar shugaban kasa ta yi zazzafan martani ga Atiku Abubakar bayan ya soke ta da gazawa wajen magance yunwa da talauci
- Bayo Onanuga, mai ba Shugaba Tinubu shawara kan tsare-tsare na yada labarai, ya ce gwamnatinsu ta samu gagarumin ci gaba
- Hadimin na Tinubu ya dora laifin matsalolin da ake fuskanta yanzu a kan gwamnatin PDP lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban kasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Atiku Abubakar bayan ya zarge ta da kasa magance yunwa da talauci.
Fadar shugaban kasan ta bayyana cewa tana alfahari da nasarorin da ta samu zuwa yanzu.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar.a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya soki gwamnatin Tinubu
A ranar Litinin, Atiku ya bayyana cewa sama da shekara biyu bayan hawa mulki, gwamnatin Tinubu ta kasa magance matsalolin yunwa da talauci.
Ya yi gargadin cewa yunwa da matsin tattalin arziki na iya haddasa tarzoma da bore, kamar yadda ya taba faruwa a wasu kasashe.
Wane martani fadar shugaban kasa ta yi?
Sai dai a martaninsa, Bayo Onanuga, ya ce Atiku da magoya bayansa, ba su san gaskiyar abin da ke gudana a kasar nan ba.
Hadimin na Tinubu ya ce ikirarin Atiku na cewa yunwa ta yi katutu a Najeriya, da kwatanta da halin da ake ciki da rikicin da aka yi a Faransa kafin juyin juya-hali a 1789 ko juyin juya-halin Bolshevik na Rasha a shekarar 1917, ba daidai ba ne.
Onanuga ya ce sabon rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ya nuna cewa hauhawar farashi ya ragu tsawon watanni biyar a jere, kuma an samu karin kudaden shiga fiye da kowane lokaci.

Kara karanta wannan
Buba Galadima: Na kusa da Kwankwaso ya fallasa makarkashiyar Tinubu kan 'yan adawa
Ya kara da cewa gwamnatoci jihohi yanzu suna iya biyan albashi da fansho a kan lokaci tare da yin ayyukan raya kasa, wanda wannan wata nasara ce da ba a taba gani ba a baya.
Shugaba Bola Tinubu ya kawo sauyi
A cewar Bayo Onanuga, bayan shekaru biyu da watanni biyar kacal a kan karagar mulki, Najeriya na ganin sauye-sauyen da su ka tabbatar da nagartar shugabancin Tinubu.

Source: Twitter
"Bayan shekara biyu da watanni biyar, muna alfahari da ci gaban da aka samu karkashin jagorancin Shugaba Tinubu."
“Atiku da magoya bayansa na iya yin watsi da wadannan nasarori, amma ’yan Najeriya suna gani kuma suna jin canjin da ake samu a fadin kasa."
- Bayo Onanuga
Bola Tinubu ya kammala hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala hutunsa na aiki da ya je yi a kasar Faransa.
Shugaba Tinubu ya kammala hutun ne kafin lokacin da aka tsara, inda ya shirya dawowa gida Najeriya don ci gaba da ayyukansa na gwamnati.
A cikin wata sanarwa da aka fitar, an bayyana cewa Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya a ranar Talata, 16 ga watan Satumban 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
