'Yan Bindiga Sun Kashe Sarkin da Suka Yi Garkuwa da Shi, Sun Jefar da Gawarsa a Daji

'Yan Bindiga Sun Kashe Sarkin da Suka Yi Garkuwa da Shi, Sun Jefar da Gawarsa a Daji

  • 'Yan bindiga sun kashe Sarkin Shuwaka na Garga da ke karamar hukumar Kanam a jihar Filato kwanaki kadan bayan sace shi
  • Kungiyar KADA mai fafutukar ci gaban yankin Kanam ta ce wannan kisa ya kara fito da matsalar tsaron da ta addabi al'umma
  • Kungiyar ta yi kira ga shugabanni su gaggauta daukar matakin da ya dace domin dawo da tsaro da kwanciyar hankali a Kanam

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Sarkin Shuwaka na Garga da ke ƙaramar hukumar Kanam a jihar Filato, Malam Hudu Barau, ya rasa ransa bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar da suka yi garkuwa da basaraken ne suka yi ajalinsa.

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato.
Hoton Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Ƙungiyar Cigaban Kanam (KADA) ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da Shugabanta, Shehu Kanam, da sakatare, Barista Garba Aliyu, suka fitar a ranar Litinin, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan ɗan sa kai ya buɗe wuta a masallaci, an samu raunuka

An gano gawar Sarkin da aka sace a Filato

A cewar ƙungiyar, ‘yan bindigar sun sace basaraken ne kimanin kwanaki shida da suka gabata, daga bisani kuma suka kashe shi ta hanyar da ta daɗa girgiza al’umma.

Kungiyar ta bayyana cewa an gano gawar Sarkin a dajin Wanka bayan 'yan bindigar sun hallaka shi.

KADA ta bayyana lamarin a matsayin babbar ankararwa kan matsalar tsaro da hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a yankunan Kanam da kewaye.

Kungiyar KADA ta zargi gwamnati da gazawa

Ta nuna takaici cewa duk da koke-koken jama’a, gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace wajen kawo ƙarshen sace-sacen mutane da kisan gilla da ake yawan yi wa jama’a.

“Mutanen Garga da yankunan da ke makwabtaka na rayuwa cikin tsantsar fargaba. Ya zama dole shugabanninmu na siyasa su dauki mataki cikin gaggawa don tabbatar da tsaron jama’a,” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta kuma bukaci Gwamna Caleb Mutfwang ya ayyana dokar ta baci a Garga tare da tura jami’an tsaro isassu domin dakile ‘yan bindigar.

Kara karanta wannan

Ambaliya ta lalata gonaki da gidaje bayan mamakon ruwan sama a Kaduna

Haka kuma, sun zargi wakilan majalisar jiha da na tarayya daga yankin da gazawa wajen kare jama’arsu daga hare-hare da kashe-kashe da suka dade suna faruwa.

Taswirar jihar Filato.
Hotom taswirar jihar Filato da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

"Hakurin jama'a ya kare" - KADA

KADA ta yi gargaɗin cewa haƙurin jama’a ya ƙare, kuma ba za su kara lamuntar yin shiru da rashin ɗaukar mataki daga shugabanni ba, cewar rahoton Daily Post.

"Ya zama dole gwamnati ta dauki mataki yanzu domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
"Muna tare da iyalan mamacin da dukkan al’ummar Garga, kuma za mu ci gaba da fafutukar kare haƙƙoƙinsu da tsaron rayuwarsu,” in ji sanarwar.

'Yan bindiga sun koma gidaje a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai farmaki yankin karamar hukumar Qua’an-Pan ta jihar Filato, sun tafka barna.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla gidaje 30 ne suka kone kurmus sakamakon hare-haren da wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka kai yankin.

Shugaban karamar hukumar, Christopher Manship, ya yi kira ga shugabannin gargajiya da addini su hada kai domin kawo karshen matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262