Lauya Ya Faɗi Illar da IMF da Bankin Duniya Suka Yi wa Najeriya a Mulkin Tinubu

Lauya Ya Faɗi Illar da IMF da Bankin Duniya Suka Yi wa Najeriya a Mulkin Tinubu

  • Babban lauya a Najeriya, Femi Falana, ya ce cire tallafin man fetur kuskure ne na tattalin arziki, wanda ya ƙara ƙuncin rayuwa
  • Falana ya zargi IMF da Bankin Duniya da yi wa tattalin arzikin Najeriya mugun kulli, karkashin Shugaba Bola Tinubu
  • Ya yi tir da matakin biyan kuɗaɗe da dalar Amurka a Najeriya, inda ya shawarci gwamnati da ta maida hankali kan ƙarfafa Naira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babban lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana, SAN, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan cire tallafin ma ida ya yi a farkon mulkinsa.

Femi Falana, SAN, ya bayyana cewa cire tallafin mai ya ƙara janyo taɓarɓarewar rayuwa, kuma babban kuskure ne ga fannin tattalin arziki.

Femi Falana ya ce cire tallafin man fetur ya jefa Najeriya a mawuyacin hali karkashin Tinubu.
Babban lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana, SAN, a cikin ofishinsa. Hoto: Femi Falana
Source: Facebook

Falana ya soki Tinubu kan cire tallafin mai

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya fadi bala'in da za a shiga da Tinubu bai cire tallafin mai ba

Da yake magana a shirin 'Siyasa a yau' na Channels TV, a ranar Lahadi, Falana ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa batun tallafin ba sabon abu ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce cire tallafin mai yana da alaƙa da tsare-tsaren IMF da Bankin Duniya da suka daɗe suna shirya wa ƙasashe masu tasowa, wadanda ke jefa mutane a talauci.

"Ni tun daga 2012, ban taba goyon bayan cire tallafin man fetur ba. Ai babu wata ƙasa a duniya da ta cire tallafi gaba ɗaya.
"Hatta manyan ƙasashen Yammacin duniya, kamar Amurka, Birtaniya, Faransa, da sauran su, suna ba da tallafin wutar lantarki, aikin gona, da sauran fannoni na rayuwar al'ummarsu."

- Femi Falana, SAN.

Falana ya cacaki IMF, Bankin Duniya

Falana ya zargi Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya da yi wa tattalin arzikin Najeriya mugun kulli, ciki har da kitsa cire tallafin da kuma karya darajar Naira.

A cewarsa, tsare-tsaren da manyan cibiyon kudin biyu suka bayar, kuma shugaban kasar ya yi amfani da su ne suka haifar da tashin hankali a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Peter Obi ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

"Muna roƙon gwamnati da ta sanar da waɗannan cibiyoyin na Yamma cewa babu wata ƙasa da ta ci nasara bisa ga tsare-tsaren cibiyoyin Bretton Woods."

- Femi Falana, SAN.

Femi Falana ya roki gwamnati ta sanya Najeriya ta zama cikakkiyar mamba a BRICS.
Babban lauyan kare hakkin dan Adam, FEmi Falana, SAN, ya na hira da 'yan jarida a cikin ofishinsa. Hoto: Femi Falana
Source: Twitter

Falana ya nemi Najeriya shiga BRICS

Babban lauyan ya kuma yi tir da yadda komai na hada hadar kuɗi a Najeriya ke son komawa kan dalar Amurka, inda ya ce abin takaici ne ace Tinubu ya ba 'yan wasan ƙwallon ƙafa kyautar daloli maimakon Naira.

Falana ya ba gwamnati shawar zama cikakkiyar mambar BRICS, wacce ya ce tana ba da damarmaki masu kyau na rage dogaro da dala da cibiyoyin kuɗi na Yamma.

“Dole ne mu tallata Naira, mu ƙarfafa ta, a kan dala, saboda Naira ita ce kuɗin ƙasarmu, ba dala ba. Yin watsi da Naira laifi ne. Laifi ne a ƙarƙashin Sashe na 20 na Dokar Babban Bankin Ƙasa.

- Femi Falana, SAN.

'Dalilin cire tallafin fetur' - Femi Falana

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Femi Gbajabiamila ya jaddada cewa cire tallafin fetur da shugaba Bola Tinubu ya yi alamar jarumta ce ta fuskar shugabanci.

Kara karanta wannan

CCT: An fadada shirin tallafin N25,000 duk wata, za a dauki karin mutum 600,000 a Najeriya

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya fadi hakan ne a taron tsofaffin 'yan majalisu na Kudancin Najeriya, wanda aka yi a Abeokuta, jihar Ogun.

Gbajabiamila ya ce jarumtar shugabancin Tinubu ta hada da cire tallafin mai, gyaran tsarin haraji da kafa hukumar NELFUND da dai sauran shirye-shirye.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com