Jagoran 'Yan Bindiga, Ado Aliero Ya Mika Wuya ga Zaman Lafiya bayan Sulhu

Jagoran 'Yan Bindiga, Ado Aliero Ya Mika Wuya ga Zaman Lafiya bayan Sulhu

  • Ado Aliero ya bayyana cewa yana da yakinin zaman lafiya zai tabbata a Katsina da sauran jihohi bayan taron Faskari
  • Taron ya haɗa manyan ƙungiyoyin ‘yan bindiga da suka yi alƙawarin rungumar zaman lafiya da zama tare da al’umma
  • Shugabanni da sauransu sun ja kunne cewa tattaunawar baya-bayan nan ta zama ta gaskiya don dakile matsalar tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Katsina - Fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Ado Aliero, ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwa zaman lafiya zai tabbata a Katsina da ma sauran sassan Najeriya.

'Dan ta'addan ya bayyana haka ne bayan wani babban taron tattaunawa da aka gudanar a karamar hukumar Faskari.

Dan ta'adda, Ado Aliero yana jawabi a taron sulhu a Katsina
Dan ta'adda, Ado Aliero yana jawabi a taron sulhu a Katsina. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan jawabin da Ado Aliero ya yi ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe jagoran 'yan ta'adda, Kachalla Babangida bayan gumurzu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron da aka bayyana a matsayin mafi girma a tarihi ya tara kungiyoyin 'yan ta'adda da dama, inda suka bayyana aniyar su ta daina rikici tare da zaman lafiya da al’umma.

A cewar Aliero, wannan zama ya fi sauran tattaunawa da aka taba yi muhimmanci saboda yawan mutanen da suka fito fili domin nuna aniyar zaman lafiya.

Tarihin kama ɗan Ado Aliero

Aliero ya tuna cewa a baya ya taba shiga irin wannan shiri na tattaunawa a Katsina, amma ya ce ƙoƙarin ya rushe bayan kama ɗansa.

Ya ce a lokacin suna rayuwa lafiya tare da hukumomi da jami’an tsaro, amma ya yanke shawarar janyewa daga zaman lafiya bayan ya tabbatar ɗansa yana tsare ba bisa dalili ba.

A cewarsa, wannan ne ya jawo shi da mabiyansa suka sake komawa aik-aikan da ya dade yana tayar da hankali a yankin.

Jawabin Ado Aliero a Katsina

A cewar Aliero, taron Faskari ya bambanta da duk wanda aka taba yi a baya, domin shi ne karon farko da yawancin shugabannin ‘yan bindiga suka bayyana fili don tattaunawa.

Kara karanta wannan

An taho daga kasar Faransa zuwa Najeriya an karrama Rabiu Kwankwaso

Ya bayyana kwarin gwiwa cewa sabon matakin zai kawo ɗorewar zaman lafiya ba kawai a Katsina ba, har ma a wasu jihohi da ke fama da matsalar rikici.

Ya fadi haka ne duk da cewa an yi irin waɗannan yarjejeniyoyi a baya amma daga bisani wasu daga cikin ‘yan bindigar suka koma tayar da rikici da satar jama'a.

Ado Aliero a wani taron domin neman zaman lafiya da aka yi a baya
Ado Aliero a wani taron domin neman zaman lafiya da aka yi a baya. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Yadda aka yi taron sulhu a Katsina

Taron na Faskari ya samu halartar shugabannin al’umma, wakilan jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Rahotanni sun bayyana cewa sun jaddada muhimmancin gaskiya da sadaukarwa wajen kawo karshen matsalar.

Shugabannin sun bayyana cewa nasarar wannan shiri zai dogara ne a kan cikakken bin yarjejeniya da kauce wa komawa ga rikici bayan ɗan lokaci.

An kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ci gaba da sanya idanu tare da tabbatar da cewa duk wata ƙungiyar ‘yan bindiga ta tsaya kan alƙawuran da aka cimma.

An kama 'yan daba da shigar mata

A wani rahoton, kun ji cewa an kama wasu matasa da ake zargi 'yan daba ne da shigar mata a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu da kansa ya fadi abubuwan da ya tattauna da shugaban Kasar Faransa

Rahotanni sun bayyana cewa an kama matasan ne a unguwar Kurna yayin da suka nufi kai hari kan jama'a.

An bayyana cewa matasan sun shiga yankin ne da nufin kisan gilla ga wasu mutane kafin a hada kai a kama su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng