'Za a Sheƙa Ruwa na Kwana 5,' An Faɗi Jihohin Arewa 10 da Za Su Gamu da Ambaliya
- Gwamnatin tarayya ta gargadi yankuna 32 a jihohi 11 kan yiwuwar ambaliya mai tsanani daga ranar 14 zuwa 18 ga Satumba, 2025
- Ma’aikatar muhalli ta ce kogin Gongola, Benue da Niger sun fara cika, lamarin da ke barazana ga al’umman da ke bakin koguna
- A bana kadai, ambaliya ta kashe fiye da mutane 231, yayin da sama da ta shafi fiye da mutum miliyan 5 a sassa daban-daban
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa wurare 32 a fadin jihohi 11 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda zai haifar da ambaliya.
Ta bakin cibiyar kula da ambaliyar ruwa ta kasa, gwamnatin ta ce za a sheka ruwa mai yawa tare da ambaliyar a tsakanin ranakun 14 zuwa 18 ga Satumba, 2025.

Source: Original
Ambaliyar ruwa za ta shafi jihohi 11
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, daraktan sashen zaizayar kasa, ambaliya da yankunan gabar teku na ma'aikatar muhalli ta tarayya, Usman Abdullahi Bokani ne ya fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar gargadin, jihohi da yankunan da za su fuskanci yiwuwar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan saman sun haɗa da:
- Adamawa: Ganye, Natubi
- Benue: Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma, Ukpiam
- Nasarawa: Agima, Rukubi, Odogbo
- Taraba: Beli, Serti, Donga
- Delta: Umugboma, Umukwata, Abraka, Aboh, Okpo-Krika
- Niger: Rijau
- Kebbi: Ribah
- Kano: Gwarzo, Karaye
- Katsina: Jibia
- Sokoto: Makira
- Zamfara: Kaura Namoda, Shinkafi, Maradun, Gusau, Anka, Bungudu
Barazanar ambaliya ga yankunan koguna
Ma'aikatar ta yi gargadi cewa karuwar ruwa a kogin Gongola, Benue, da kuma Neja na iya haifar da ƙarin haɗari, inda ta yi kashedi ga al'ummomin da ke zaune a yankunan kogunan.
Jaridar Punch ta rahoto daraktan sashen kula da ambaliyar, Usman Bokani, ya ce:
"Haka kuma, saboda karuwar ruwa a kogunan Gongola, kogin Benue, da kogin Neja, ana shawartar al'ummomin da ke cikin kwazazzabai da su gaggauta yin kaura.
“Lallai, mutanen da ke zaune a bakin koguna su gaggauta barin garuruwansu domin tsira da rayukansu. Sannan hukumomi su dauki mataki cikin gaggawa don rage illar ambaliyar.”

Source: Getty Images
Tasirin ambaliyar ruwa a baya-bayan nan
Wannan gargadin na zuwa ne kwanaki bayan ruwan sama mai yawa a Zariya, jihar Kaduna, ya tilasta yara 470 barin gidajensu tare da rusa gidaje 270.
Kididdigar hukumar NEMA ta nuna cewa daga ranar 4 ga Satumba, ambaliya ta kashe mutane 231, inda wasu 114 suka bace, sannan mutane 607 suka jikkata.
A bara, ambaliya ta shafi mutane sama da 5.2m a jihohi 35 da kananan hukumomi 401, ta raba mutane sama da 1.2m da muhallansu, ta kashe 1,237 tare da jikkata fiye da 16,000.
Ambaliyar ruwa ta yi barna a jihohi 31
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ambaliyar ruwa ta lalata hekta 180,000 na gonaki a jihohi 31 kuma hakan ya shafi mutane miliyan 1.2.

Kara karanta wannan
'Ku zama cikin shiri,' NiMet ta fadi jihohi 4 da ambaliya za ta shafa ranar Juma'a
Rahoton SBM Intelligence ya nuna cewa mutane miliyan 2.2 sun rasa muhallansu, yayin da aka samu hauhawar farashin abinci saboda ambaliya.
A cikin rahoton, SBM ya nuna cewa sauyin yanayi da rashin tsaro sun addabi manoma Najeriya, musamman a jihohi 31 na kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

