Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Sojan Bogi da Ya Damfari Mutane Fiye da N1m

Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Sojan Bogi da Ya Damfari Mutane Fiye da N1m

  • ‘Yan sandan Ondo sun kama Abdullahi Saliu wanda ya yake sojan gona da Kanal a rundunar soji yana damfarar mutane kudi
  • An gano cewa ya damfari mata biyu ne da sunan zai saka ‘ya’yansu a aikin hukumar Kwastam da Immigration, inda ya karɓi N1.3m
  • Rundunar ‘yan sanda ta ce ya dade yana wannan sana’a a jihohi daban-daban, kuma yanzu haka an gurfanar da shi a kotun majistire

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da cafke wani mutum da ya dade yana damfarar mutane da sunan jami’in soja.

Mutumin mai suna Abdullahi Saliu ya sa ya zama babban jami’in soji, inda ya damfari mutane sama da ₦1.3m ta hanyar yin alkawarin samar musu da aiki a hukumomin gwamnati.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe jagoran 'yan ta'adda, Kachalla Babangida bayan gumurzu

'Yan sanda sun kama Abdullahi Saliu da ya dade yana damfarar mutane da sunan jami'in soja.
Jami'an 'yan sanda na sashen yaki da ta'addanci a bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An cafke sojan bogi da ke damfar mutane

DSP Ayanlade Olayinka Olushola, mai magana da yawun rundunar ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya fitar a shafin rundunar na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa:

“Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta kama wani Kanar din soja na bogi, mai suna Abdullahi Saliu, mazaunin otel din Top Quality.
"Abdullahi ya yi kaurin suna wajen sojan gona da Kanal a cikin sojojin Najeriya, inda ya damfari mutane sama da N1.3m.”

Sojan bogi ya damfari mata N1.3m

A cewar sanarwar da aka wallafa a ranar Lahadi, wanda ake zargin “ya yaudare wasu mata su biyu, Oshoade Janet da Daisi Remilekun Joy, da sunan zai sama wa 'ya'yansu aiki a hukumar Kwastam da ta shige da fice ta Najeriya.”

Sanarwar ta kara da cewa:

"Abdullahi Saliu ya karbi kudi N1,377,000 daga matan don sama wa 'ya'yansu aiki, amma daga bisani, ya yi amfani da kudin wajen biyan bukatar kansa."

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin Ministan Tinubu da gwamna a APC? An samu bayanai

Masu bincike sun Abdullahi Saliu a matsayin wani dan damfara da ya dade yana gudanar da ayyukansa na damfara a jihohi daban-daban.

“Bincike ya kara bayyana cewa ayyukan wanda ake zargin sun kai har jihohin Edo, Delta, Kogi, da Ondo."
'Yan sanda sun gurfanar da sojan bogi a kotu, ya damfaru mutane N1.3m.
Taswirar jihar Ondo, da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An gurfanar da sojan bogi a kotu

Sanarwar ta ce Abdullahi ya dade yana sojan gona da manyan jami'an tsaro yana damfarar mutane ta sigogi daban daban, har sai yanzu da aka kama shi.

DSP Ayanlade Olayinka Olushola ya ce:

"Ya kasance yana bayyana kansa a matsayin jami’in sojan ruwa, babban jami’in hukumar shige da fice, da na hukumar Kwastam, duk don yaudarar ‘yan kasa masu neman aiki.”

A yanzu an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistire ta Ondo, inda ake tuhumarsa da aikata damfara da kuma sojan gona da jami’an tsaro.

DSP Olushola ya bayyana cewa cafke Abdullahi Saliu na daga cikin nasarorin da rundunar ta samu a baya-bayan nan wajen yaki da aikata laifuffuka.

An cafke sojan bogi Fatakwal

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojoji sun cafke wani matashin da ke ikirarin shi soja ne a Fatakwal, birnin jihar Rivers da ke cutar mutane.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama wiwi mai nauyin kilo 112 a wajen hadarin mota a Kano

Wanda ake zargin mai suna Desmond Okehdan, wanda dan asalin jihar Anambra ne, ya dade yana cutar mutane da kuma damfararsu.

Desmond Okehdan ya bayyana cewa sha'awar aikin soja ne ya sa shi ya ke aikata hakan saboda yadade ya na nema bai samu ba tun 2016.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com