Maryam Shetty Ta Shirya Gasar Alkur'ani, Ta ba da Kyautar Sama da Naira Miliyan 1.75

Maryam Shetty Ta Shirya Gasar Alkur'ani, Ta ba da Kyautar Sama da Naira Miliyan 1.75

  • Fitacciyar matashiyar Arewa, Maryam Shetty, ta shirya gasar karatun Alƙur’ani a kafar Facebook wacce ta ja hankalin dubban matasa
  • Hajiya Mariya Sanusi Dantata, mahaifiyar Alhaji Aliko Dangote, ta halarci bikin karshe inda aka yi addu’a domin zaman lafiya ga Najeriya
  • Nuraddeen Mu’azu daga Abuja ya zama zakaran gasar, inda ya samu kyautar N1m, yayin da masu biye da shi suka ci N500,000 da N250,000
  • Wasu da Legit Hausa ta zanta da su, sun yaba da wannan gasa da Shetty ta sanya, suna masu cewa, mataki ne na karfafa ilimin addini

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Dr. Maryam Shetty, tsohuwar zababbiyar minista a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ta gudanar da gasar karatun Alƙur’ani a Kano, irinta ta farko da ta fara a intanet.

An gudanar da gasar ne ta shafin Facebook ɗinta, inda dubban mahalarta daga sassa daban-daban na ƙasar suka aika da bidiyon su suna karatun Alƙur’ani.

Kara karanta wannan

'Za mu fitar da Tinubu daga Aso Rock Villa,' Aregbesola ya fadi shirin ADC a 2027

Maryam Shetty ta shirya gasar Alkur'ani a Facebook, inda ta raba kyautar N1.752m
Dr. Maryam Shetty ta shirya gasar karatun Alkur'ani mai girma, ta raba fiye da miliyan 1.7. Hoto: Fred de Noyelle/Getty Images, Maryam Shetty/Facebook
Source: UGC

Maryam Shetty ta shirya gasar Alkur'ani

Kwamitin tantance gasar karatun Alƙur’ani na kasa (NQRCC) ne ya duba bidiyon sannan ya fitar da zakarun gasar, a cewar rahoton Tribune.

Yayin da take bayyana manufar gsar, Dr. Maryam Shetty ta ce tana son mayar da kafafen sada zumunta wajen ibada da tunani mai kyau, maimakon bata lokaci da shashanci.

Maryam Shetty ta ce:

“Maimakon barin TikTok da Instagram su zama wajen shashanci, me zai hana mu maida su wurin ibada, koyon kyawawan dabi’a da tunani mai zurfi?”

Ta ƙara da cewa shirin gasar, da aka lakaba masa suna #ReciteWithShetty, ba wai kawai gasa ba ce, amma wani yunkuri ne da ya sake ƙara ƙaunar Alƙur’ani ga matasa.

“Abin da ya fara a matsayin ƙaramin shiri ya koma babban al'amari da ya kama zukatan matasan Arewacin Najeriya da ma kasa baki daya. Karatuttukan da suka yi sun yadu kamar wutar daji.”

Kara karanta wannan

'Dan Majalisa, Adamu Aliyu ya aikata laifi mai girma, kotu ta ayyana nemansa ruwa a jallo

- Dr. Maryam Shetty.

An yi wa kasa addu'a a taron Maryam

Dr. Maryam Shetty ta gode wa shugabannin addini, tsofaffin shugabannin ƙasa da kuma sarakunan gargajiya da suka nuna gasar a matsayin alama ta farfaɗo da dabi’u da al’adu.

Hajiya Mariya Sanusi, mahaifiyar Alhaji Aliko Dangote, ta yaba da kokarin Dr. Shetty inda ta yi kira ga matasa su yi amfani da damar karatu, sannan ta yi addu’ar zaman lafiya ga Najeriya.

Mahalarta taron, sun taru sun yi wa kasa addu'a, tare da addu'ar Allah ya sanya albarka a gasar, ya kuma kara wa wacce ta shirya gasar kwarin gwiwa, tare da ba ta lada mai yawa.

Maryam Shetty ta ce za ta ci gaba da shirya gasar karatun Alkuri'ani a shafinta na Faceboo.
Dr. Maryam Shetty, tsohuwar zababbiyar minista a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Maryam Shetty
Source: Facebook

Zakarun gasar Alkuri'ani sun samu kudi

  • Zakara: Nuraddeen Mu’azu daga Abuja ya samu maki 97.6 tare da kyautar N1m.
  • Na biyu: Muhammad Khalid Idris daga Bauchi ya samu maki 97.4, ya samu kyautar N500,000.
  • Na uku: Aisha Tahir Idris daga Jigawa ta samu maki 97, an ba ta kyautar N250,000.

Kara karanta wannan

2027: Malaman Musulunci sun yi ruwan addu'o'i ga Tinubu da Barau a Kano, an yi yanka

Dr. Maryam Shetty ta bayyana cewa ita da tawagarta suna kan hanya wajen fadada shirin gasar karatun Alkur'ani domin ya zama aikin rayuwa da zai ci gaba da tallafa wa 'yan Adam.

An yaba da kokarin Maryam Shetty

Sada Bn Sulaiman, wani shahararre a Facebook, ya shaida wa wakilin Legit Hausa cewa:

"Ta yi kokari sosai, wannan abin a yaba ne. Da ire-irenta, wadanda suka shahara a siyasance da kuma a shafukan sada zumunta za su rika yin haka, da an rage 'yan nanayen TikTok.
"Akwai mutane masu ilimi, masu son nuna baiwarsu, amma suna jin tsoron shafukan sada zumunta, amma irin wannan gasa, za ta sa su fito su nuna bajintarsu. Gaskiya ta yi kokari sosai."

Malam Nura Mailafia, malamin Islamiyya a Katsina, ya ce ya kwana biyu bai ga abin da ya burgesa a soshiyal midiya ba irin wannan gasa.

"Wallahi ni na yi mamaki, ban dauka irin za ta wani sanya kyaututtuka masu tsoka har haka ba. Har ina fada ma wani cewa, ita wannan ta dauko aikin yada da'awah.
"Abin gwanin sha'awa. Kuma abin da ya kara ma abin armashi, ka ga dama sananna ce, don haka sai gasar ta yadu a ko ina. Na ji dadi da na ga Hafizai suna turo karatuttukansu."

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da 'yar takarar PDP a kotu kan zargin sabawa doka

Malam Nura ya roki Maryam Shetty da cewar, nan gaba, ta ware wata gasar ta mata zalla, wanda hakan zai kara zaburar da mata wajen dagewa a Hadda.

Maryam Shetty ta magantu kan mukamin minista

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Maryam Shetty ta yi magana a karon farko bayan Shugaba Bola Tinubu ya maye gurbinta a mukamin minista.

Matashiyar na ɗaya daga cikin ministoci 19 da Tinubu ya naɗa amma a ranar Jumu'a ya janye sunanta kana ya maye gurbin da mutum biyu.

Sauya fitacciyar matashiyar 'yar siyasar, ya haddasa kace nace a kafafen sada zumunta amma Maryam ta ce tana godiya da duk matakin da Tinubu ya ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com