Za Ayi Nasara, Gwamna Dikko Radda Ya Fadi Babbar Hanyar Kawo Karshen Ta'addanci
- Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa ingantaccen ilimi na daya daga cikin manyan hanyoyin magance matsalolin tsaro a Arewa
- Gwamnan na Katsina, ya ce gwamnatinsa ta zuba jari mai yawa a fannin ilimi, ciki har da tallafa wa ƙungiyoyin da ke habaka ilimi
- Ya ce gwamnatinsa ta kaddamar da makarantu na musamman uku, yayin da dalibai da dama ke samun tallafin karatu a ƙasashen waje
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ilimi shi ne ɗaya daga cikin manyan makamai na yaki da rashin tsaro.
A cewar Gwamna Dikko Radda, da ilimi ne za a magance matsalar rashin tsaro daga tushe, kamar dai ace a tuge jijiyar bishiya don kashe ta gaba daya.

Source: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Hanyar magance matsalar tsaro' - Gwamna Radda
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan na Katsina ya ce:
“Ilimi mai inganci na taka muhimmiyar rawa wajen yaki da rashin tsaro ta hanyar rage talauci, jahilci da rashin aikin yi.
"Yana bai wa mutane kwarewa da basira da dabi’u masu kyau domin samar da tunani mai zurfi, haƙuri da ɗabi’ar zama ɗan ƙasa nagari.”
Ya ƙara da cewa al'ummar da ta samu ingantaccen ilimi na iya guje wa yaudarar miyagun mutane, tsattsauran ra’ayi da tashin hankali.
Haka kuma, ilimi na taimakawa wajen ƙarfafa haɗin kai a cikin al’umma, bunƙasa tattalin arziki da kuma gina ƙwararrun cibiyoyin gwamnati da ake buƙata domin dorewar zaman lafiya da tsaro.
Gwamna Radda ya saka hannun jari a ilimi
Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa gwamnatin sa na ci gaba da zuba jari a fannin ilimi ta hanyoyi daban-daban.
Ya ce gwamnati na tallafawa shirye-shiryen ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke taimakawa wajen ƙara samun damar karatu, musamman a yankunan karkara.
Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da Dan Amana Tested and Trusted Initiative a Katsina, inda ya jaddada cewa manufar gwamnatin sa ita ce “Gina makomarka ta hanyar ilimi."
Ya kuma bayyana cewa tun farkon mulkinsa gwamnatin ta tura yara daga Katsina zuwa kasashen waje domin karatu a fannonin da ake buƙata.
“Mun tura yara karatu a fannin likitanci a Misira da kirkirarriyar fasa ta AI a China bisa cancanta. Ina alfahari da cewa suna yin fice a fannoni daban-daban,” in ji Dikko Radda.

Source: Twitter
Shirye-shiryen makarantu na musamman
Radda ya sanar da kafa shirin Makarantu na Musamman a Katsina, wanda ya haɗa da gina makarantu na zamani a Radda, Jikamshi da Dumurkul.
Ya ce makarantun za su zama cibiyoyin gano yara masu kaifin basira a Katsina, kuma za a dauki dalibai da malamai bisa cancanta kadai, ba tare da la’akari da asalinsu ko matsayinsu na zamantakewa ba.
A cewar gwamnan, waɗannan tsare-tsare na nuna jajircewar gwamnatin Katsina wajen ɗaga matsayin ilimi, karfafa nagarta da samar da ci gaban da zai dore a jihar.
Gwamna Dikko Radda ya lashe zambar yabo

Kara karanta wannan
Sabon tarihi: Dubban 'yan auren jinsi sun gudanar da ziyarar bauta a Vatican a karon farko
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa ya lashe lambar yabo ta gwamnan da ya fi kowane aiki a shekarar 2025.
Kamfanin Aso Multimedia ne ya ba Gwamna Radda wannan lambar yabo domin yabawa kokarin da yake wajen kawo ci gaba a jihar Katsina.
Kwamishinar harkokin mata ta Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta faɗi wasu daga cikin ayyukan da Dikko Raɗɗa ya yi a shekaru biyu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

