An Taho daga Kasar Faransa zuwa Najeriya an Karrama Rabiu Kwankwaso
- Tawaga daga ƙungiyar ’yan Najeriya a Faransa ta kai ziyarar girmamawa ga Rabiu Musa Kwankwaso a Abuja
- A yayin ganawar da suka yi, tawagar ta mika masa lambar yabo saboda gudummawarsa a fannin ilimi da gina mutane
- Daya daga cikin wadanda suka zo daga Faransa ya nuna wa Kwankwaso shaidar karatu bayan ya kammala digirin PhD
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi tawagar ’yan Najeriya mazauna Faransa a gidansa da ke Maitama, Abuja.
Tawagar, wacce Haruna Ibrahim Rogo ya jagoranta, ta bayyana ziyarar a matsayin girmamawa ga namijin ƙoƙarin Kwankwaso wajen ƙarfafa matasa da ilimi.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai kan yadda ziyarar ta gudana ne a wani sako da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X.

Kara karanta wannan
Ganduje ya kafa kwamiti, zai binciki gwamnatin Kano kan korar kwamandojin Hisbah 44
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, tawagar ta gabatar masa da lambar yabo domin nuna godiya da jinjina ga rawar da yake takawa wajen raya al’umma.
An karrama Rabiu Kwankwaso daga Faransa
Haruna Rogo ya bayyana cewa lambar yabon da aka mika wa tsohon gwamnan Kano na nuna yadda ’yan Najeriya a ƙasashen waje ke jin daɗin irin gudummawar da ya ke bayarwa.
Ya ce Kwankwaso ya kasance jagora mai kishin ci gaban matasa da ɗaukar nauyin ilimi, wanda hakan ya jawo sha’awar mazauna ƙasashen waje su nuna godiya.
Wani ya nuna wa Kwankwaso shaidar karatu
A yayin taron, Haruna Rogo ya gabatar da takardar shaidar digirin Ph.D. daga Jami’ar CY Paris, inda ya bayyana kansa a matsayin wanda ya amfana da shirin tallafin karatu na Kwankwasiyya.
Ya ce tallafin ya ba shi damar yin karatu a ƙasashen waje har ya cimma burinsa, abin da ya nuna tasirin shirin ga matasan Najeriya.

Source: Facebook
Tsarin tallafin karatun Kwankwasiyya
Shirin Kwankwasiyya tallafin karatun Kwankwasiyya ya daɗe yana ɗaukar nauyin ɗalibai daga Najeriya zuwa ƙasashen waje.
An kafa shi da manufar ƙarfafa ilimi, inganta nagartaccen shugabanci da kuma karfafa gwiwar mata da matasa a fannoni daban-daban.
Kwankwaso, wanda ya kafa shi, ya yi shi ne manufar samar da ingantaccen ilimi domin ciyar da jihar Kano da kasa baki daya gaba.
Shirin tallafin ya samu karbuwa sosai a jihar Kano, inda ta kai ga cewa Rabiu Kwankwaso ya taba sayar da kadarorinsa ya tura dalibai karatu waje.
Bayan zuwan Abba Kabir Yusuf karashin jam'iyyar NNPP a 2023, gwamnan ya daura daga inda Kwankwaso ya tsaya wajen cigaba da tura dalibai karatu ketare.
Benue: Hausawa sun gana da Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa Hausawa da sauran 'yan Arewa da ke kasuwancin sayar da lemo a jihar Benue sun gana da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ganawar da suka yi ta mayar da hankali ne kan matsalolin da 'yan kasuwar ke yawan fuskanta a jihar, wanda hakan har ya kai ga yin yajin aiki.
Bayan ganawarsu, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi alkawarin isar da kukansu wajen gwamnatin jihar Benue kai tsaye domin samar musu da mafita da saukaka kasuwancinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

