Kadarorina na saida, mu ka tura Matasa 370 karatu zuwa kasashen waje inji Kwankwaso

Kadarorina na saida, mu ka tura Matasa 370 karatu zuwa kasashen waje inji Kwankwaso

- Rabi’u Kwankwaso ya tarbi matasa 370 da aka tura karatu a kasashen waje

- Kwankwasiyya Development Foundation ta dauki nauyin karatun matasan

- Kwankwaso yace sai da ya sa wasu kadarori a kasuwa domin a samu kudi

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bada labarin yadda ya saida wasu kadarori da ya mallaka domin ganin matasa sun yi karatu.

Jaridar Vanguard ta rahoto Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya na wannan jawabi a lokacin da ya yi maraba da matasan da aka tura zuwa karo karatu a ketare.

A karshen makon nan ne yaran Kanon da gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation ta dauki nauyinsu, su ka dawo daga Indiya, Dubai da Sudan.

Wadannan matasa sun dawo gida ne ta babban filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano.

KU KARANTA: Rashin gaskiya ta sa na ajiye aiki a NDDC - Kwankwaso

Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi farin ciki da ganin wadannan Bayin Allah da gidauniyarsa ta dauki nauyin karatunsu, sun kammala digirgir, sun dawo Najeriya.

A cewar tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, sun iya aika matasan su karo karatu ne bayan sun samu gudumuwa daga wuraren mutane daban-dabam.

“Wannan rana ce mai tarihi, abin da mu ke buri ya tabbata. Ina farin cikin dawowarku gida, na yi murna da wasu da yawa su ka samu sakamako mai kyau.” Inji Kwanwaso

“Yadda na ke ganin darajar ilmi ta wuce duk inda ake tunani, sai da ta kai na saida wasu daga kadarorin da na mallaka domin a fara wannan shiri ta gidauniyar Kwankwasiyya.”

KU KARANTA: Ganduje da ya yi wa Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar Mahaifinsu

Kadarorina na saida, mu ka tura Matasa 370 karatu zuwa kasashen waje inji Kwankwaso
Wasu cikin Matasan da karatu Hoto: nairaland.com
Source: UGC

Sanata Kwankwaso ya cigaba: “Dalibai 370 aka ba tallafin karatu wanda ya hada da kudin makaranta, kudin jirgi, wurin zama, da kudin kashewa har su ka gama.”

A 2019 ne Kwankwasiyya Foundation ta shirya bikin karbar gudumuwar kudi domin aika yaran na jihar Kano zuwa jami’o’i na kasar waje, kuma attajirai sun bada gudumuwa.

Idan ba ku manta ba, a a karkashin tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso an samu fiye da Miliyan 80.

Kadan daga ciki: Alhaji A.A Rano ya bada gudumuwar Naira miliyan 30, Abdussamad Isiyaka Rabiu ya bada Naira miliyan 20, Injiniya Sagir Koki ya bada Naira miliyan 5.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel