Donald Trump Ya Sha Alwashin Hana Tinubu Samun Tazarce a 2027? Gaskiya Ta Fito
- Wani bidiyo da aka wallafa a intanet, ya nuna cewa shugaban Amurka, Donald Trump zai tsoma hannu a zaben Najeriya na 2027
- Wanda ya dauki bidiyon ya yi ikirarin cewa Trump baya son Shugaba Bola Tinubu kuma zai yi duk mai yiwuwa don hana shi tazarce
- Sai dai, wani bincike da aka gudanar ya nuna akasin wannan ikirari, kuma an warware rudanin da aka samu game da bidiyon
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Zaben Najeriya na gaba zai gudana ne a shekarar 2027, kuma tuni jam'iyyun siyasa suka fara wasa wukakensu, ana jiran a buga gangar siyasar.
A irin wannan lokaci ne, ake samun yawaitar labaran karya, inda masu amfani da soshiyal midiya kan rika yada bayanan karya domin juya sauya ra'ayoyin jama'a.

Source: Getty Images
'Trump zai hana Tinubu tazarce' - Arangee
Yayin da ake tunkarar babban zaben na 2027, wani mai amfani da Facebook, Onyee Arangee, ya wallafa wani faifan bidiyo na mintuna uku da ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban Amurka Donald Trump zai tsoma baki a zaben Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar mai magana a bidiyon, Trump baya son Shugaba Bola Tinubu kuma ya sha alwashin yin duk abin da zai iya domin ya hana shi yin tazarce.
Bidiyon ya samu karbuwa sosai inda ya tara 5,500 likes, 325 comments, 446 shares da kuma sama da kallo 25,000.
Bincike ya fallasa gaskiya
Rejoice Taddy, ta shafin Dubawa, ta gudanar da bincike domin gano sahihancin wannan ikirari, na cewar Donald Trump zai kitsa faduwar Tinubu a zaben na 2027.
Abin da aka gano shi ne cewa babu wata shaida daga manyan kafafen labarai a Najeriya ko na kasashen waje da ta nuna Trump ya yi irin wannan furuci.
Duk bayanansa na baya-bayan nan sun fi karkata kan batun shige da fice a Amurka, muhawarar tattalin arziki, da kuma shari’o’in da yake fuskanta a cikin gida.
Haka kuma, an gano cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka danganta Trump da siyasar Najeriya ba.
A baya an yada wani tsohon bidiyo da aka sarrafa da AI, inda aka nuna kamar yana magana kan shugabancin Tinubu, amma daga baya aka gano tsohuwar hirararsa ce da NBC aka yi wa wankiya.

Source: Getty Images
Trump bai ce zai hana tazarcen Tinubu ba
Babu wata hujja da ta tabbatar da cewa Donald Trump ya nuna cewa zai sanya hannu a zabukan Najeriya ko kuma nuna adawa da shugabancin Bola Tinubu.
Duk wani ikirari da aka yada a kan wannan batu karya ne kuma ya fito daga bayanan bogi da aka kirkira a kafafen sada zumunta.
Donald Trump ya ki gayyatar Tinubu taro
A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya ce ƙin gayyatar Najeriya a taron kasashen Afirka biyar da Donald Trump zai yi wulakanci ne ga Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Sabon tarihi: Dubban 'yan auren jinsi sun gudanar da ziyarar bauta a Vatican a karon farko
Ya ce rashin gayyatar ba kuskure ba ne, illa hukunci ne mai zafi kan gazawar Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce Bola Tinubu ya lalata martabar Najeriya a idon duniya, inda ya jaddada cewa ADC na shirin ceto ƙasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

