Majalisa Ta Kara Wa Gwamna Karfi, Ta Sauya Dokar Nadawa da Sauke Sarki daga Mulki
- Majalisa ta amince gwamnan Adamawa ya nada shugaban riko idan Sarki ko Hakimi ya kwanta rashin lafiya ko kuma ya gaza aiki
- Hakan na kunshe ne a kudirin da Majalisar ta amince da shi wanda ya yi wa dokar nadawa da sauke sarakuna gyara a Adamawa
- Dokar ta tanadi cewa duk wanda aka nada a matsayin Sarki ko Hakimin rikon kwarya zai sauka idan basaraken ya samu lafiya ko ya dawo aiki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa - Majalisar Dokokin Adamawa a ranar Alhamis ta amince da kudirin da ya yi gyara ga Dokar Nada da Sauke Sarakuna ta Jihar mai lamba 20 ta 2025.
Sabuwar dokar dai ta bai wa gwamna karfin ikon nada wani dan gidan sarauta ya rike mukamin Sarki ko hakimi idan wanda ke kan mulki na fama da rashin lafiya ko ya gaza gudanar da aikinsa.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Majalisar ta zartar da dokar ne bayan karbar rahoto daga kwamitin wucin gadin da ta kafa domin gyaran dokokin masarautu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gyara dokar masarautun Adamawa
Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Mohammed Buba Jijiwa ne ya jagoranci kwamitin kuma ya gabatar da rahoton aikin da aka ba su a zaman jiya Laraba.
A cikin rahoton, kwamitin ya ba da shawarar a sauya taken kudirin zuwa:
“Dokar da ta shafi tsarin nadin sarakunan gargajiya a Jihar Adamawa da kuma samar da ka’idojin nada mai rikon mukami idan Sarki ko hakimi ya kasa gudanar da ayyukansa.”
Kwamitin ya kara da cewa majalisar masarauta tare da shawarar gwamna za su iya nada wanda zai rike mukamin Sarki ko Hakimi har sai wanda ke kan karaga ya warke.
“Wanda aka nada zai karɓi dukkan ayyuka da nauyin da suka rataya a wuyan Sarki ko Hakimin da ke fama da rashin lafiya,” in ji rahoton.
An kara ba gwamna karfi wajen nadin Sarakuna
Haka kuma rahoton ya bayyana cewa nadin mai rikon kwara zai kare idan asibitin gwamnati ya tabbatar da cewa Sarkin ko Hakimin da ya kamu da rashin lafiya ya warke.
"Idan Sarki ko Hakimi ya gaza halartar manyan ayyukan gwamnati sau uku a jere cikin shekara guda saboda rashin lafiya, masarauta tare da shawarar gwamna, za su iya nada shugaban riko kamar yadda aka tanada a sashe na 6 na dokar."

Source: Facebook
Yadda Majalisa ta amince da dokar
Bayan rahoton ya samu karɓuwa, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa, Kate Raymond Mamuno (Demsa), ya nemi a yiwa kudirin karatu na uku.
Kuma nan take, Hon. Haruna Jilantikiri, mai wakiltar mazabar Madagali, ya mara masa baya.
Daga nan Kakakin Majalisa, Bathiya Wesley, ya sanar da amincewa da kudirin tare da ba da umarnin a tanadi kwafi domin mika wa gwamna ya sa hannu.
Gwamnan Adamawa zai dauki ma'aikata
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin daukar matasa 12,000 aiki.
Gwamna Fintiri ya ce za a debi ma'aikata ne kafin watan Disamba 2025 a wani bangare na kokarin da gwamnatinsa take yi wajen yaki da zaman lashe wando.
Ya kara da cewa wannan kari ne a kan daukar wasu ma’aikata 5,000 da ake yi a yanzu, wanda ke nufin jimillar sababbin ma'aikatan za su kai 12,000.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


