A Karshe, Likitoci Sun Shiga Yajin Aiki, Sun Rufe Asibitocin Gwamnati Baki Daya

A Karshe, Likitoci Sun Shiga Yajin Aiki, Sun Rufe Asibitocin Gwamnati Baki Daya

  • Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki (NARD) ta umarci mambobinta su rufe asibitocin gwamnati daga ranar Juma’a
  • Likitocin sun zargi gwamnatin tarayya da gaza cika alkawarinta na biyan bukatunsu duk da wa’adin kwana 11 da NARD ta ba ta
  • Kasancewar NARD ce ke da mafi yawan likitoci a kasar nan, ana fargabar yajin aikin zai jefa marasa lafiya cikin garari a Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki (NARD), ta tsunduma yajin aiki a duk fadin Najeriya daga yau Juma'a, 12 ga Satumba, 2025.

Wannan ya biyo bayan karewar wa’adin sa’o’i 24 da suka ba gwamnati domin biyan bukatunsu, bayan wani wa’adin kwana 10 da ya shude a ranar 10 ga Satumba.

Likitoci karkashin kungiyar NARD sun shiga yajin aiki bayan gwamnati ta gaza cika alkawari.
Shugaba Bola Tinubu yana sanya hannu kan wasu takardu a fadar shugaban kasa, da likitoci suna karbar rantsuwar kama aiki a Abuja. Hoto: @DOlusegun, @nard_nigeria
Source: Twitter

Likitocin da ke karkashin NARD su ne mafi yawan ma’aikata a asibitocin koyarwa da asibitoci na musamman a fadin Najeriya, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnati ta bankado ma'aikatan bogi a Bauchi, za su fuskanci hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatun da likitoci suka gabatarwa gwamnati

Kungiyar NARD ta ce ta dauki wannan mataki saboda gwamnati ta gasa magance matsalolin da suka shafi albashi, walwala da kuma yanayin aikin likitoci.

Daga cikin bukatun da NARD ke nema akwai biyan kudin tallafin horo ga likitoci masu neman kwarewar aiki (MRTF) na shekarar 2025, da kuma biyan bashin watanni biyar daga karin albashin likitoci (CONMESS) da aka sanar.

Ƙungiyar ta kuma bukaci a biya kudin kayan aiki na shekarar 2024, a ci gaba da raba alawus na musamman ga likitoci, da kuma a maido da sahihancin shaidar karatun likitocin Yammacin Afrika.

Haka kuma sun nemi a bayar da takardun shaida ga duk wadanda suka cancanta daga kwalejin kiwon lafiya ta kasa (NPM).

Baya ga haka, suna bukatar gwamnati ta aiwatar da karin albashin likitoci na 2024, ta kuma warware matsalolin walwala da ke damun likitoci a jihar Kaduna da asibitin LAUTECH da ke a Ogbomoso.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi gargadi bayan luguden wutan Isra'ila a Qatar da jiragen yaki

Likitoci sun shiga yajin aiki a Najeriya

Shugaban NARD, Dr. Tope Osundare, ya bayyana takaicinsa kan yadda gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na magance matsalolin kungiyar, har wa'adin da aka bata ya kare.

An rahoto Dr. Osundare ya ce:

“Abin takaici shi ne, ba a cika bukatun mu ba, har wa’adin da muka bayar ya cika. Don haka, kamar yadda NEC ta umarta, mun shiga yajin aiki tun da safiyar Juma'a."

Da aka tambaye shi ko yajin aikin na gargadi ne, ya ce:

“Mu dai yanzu mun shiga yajin aiki, za mu jira matakin gwamnati, shi zai yanke hukuncin ko na gargadi ne, ko na sai baba ta gani ne."
Likitoci sun ce yajin aikin na gargadi ne, kuma za su iya zarce wa idan gwamnati ba ta biya bukatunsu ba.
Hoton likitoci, tsaye a gaban wani asibiti. Hoto: @nard_nigeria
Source: Twitter

Yajin aikin gargadi na kwana 5

Sai dai kuma, Legit Hausa ta ci karo da wata sanarwa da aka wallafa a shafin NARD na X a safiyar yau, inda ta nuna cewa yajin aikin na kwanaki biyar ne suka shiga.

Kara karanta wannan

Majalisa na barazanar hada minista da Tinubu kan 'raina' 'yan Najeriya da suka yi hadari

Sanarwar ta ce:

"Kungiyar NARD na sanar da dukkanin mambobinta da cewa yajin aikin gargadi na kwanaki biyar ya fara aiki daga yau, bisa hukuncin da NEC ta yanke.
"Muna fatan dukkanin mambobinsu a kowanne asibiti za su kauracewa aiki, tare da bin umarnin yajin aiki.
"An shiga wannan yajin aikin ne domin jaddada bukatunmu na samar da walwala, inganta yanayin aiki da bunkasa tsarin kiwon lafiya a Najeriya."

Ana fargabar cewa sabon yajin aikin na iya durkusar da harkokin kiwon lafiya a Najeriya, inda marasa lafiya da dama ke dogaro da likitocin a asibitocin gwamnati da na koyarwa.

NARD: Likita ya mutu saboda gajiyar aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani likita ya mutu sakamakon gajiya daga aikin da ya yi na kwanaki uku a jere ba tare da hutawa ba a RSUTH.

Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki (NARD) ta koka kan yadda ake cika wa mambobinta aiki a asibitocin da ke a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kungiyar TUC ta ja daga, ta ba gwamnatin Tinubu kwanaki 14 ta janye harajin fetur

NARD ta ce mutuwa saboda gajiya daga aiki babu hutu bai yi mata dadi ba, inda ta fito ta sake kira ga gwamnati kan ayyukan da ake dora wa likitoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com