Matukan Jirgin Sama Sun Sha Giya da Kwaya, Sun Kusa Halaka Mutane a Najeriya

Matukan Jirgin Sama Sun Sha Giya da Kwaya, Sun Kusa Halaka Mutane a Najeriya

  • Hukumar binciken hatsari ta NSIB ta tabbatar da cewa wasu matukan jirgin Air Peace sun sha giya da kuma kwayoyi
  • Rahoton wucin gadi ya nuna cewa jirgin ya sauka ba bisa ƙa’ida ba inda ya kauce daga hanya yayin da yake ɗauke da fasinjoji 103
  • NSIB ta ce ta bayar da umarnin gaggawa ga kamfanin jirgin domin ƙara tsaurara tsare-tsaren tsaro a dukkan tafiye-tafiye

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Hukumar NSIB ta gano cewa wasu matukan jirgin Air Peace sun yi amfani da giya da kuma wasu kwayoyi kafin jirgin su ya yi mummunar sauka a filin jirgin saman Rivers.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, lokacin da jirgin Boeing 737 ya kauce daga hanya bayan sauka, lamarin da ya jawo firgici ga fasinjoji.

Kara karanta wannan

Ana kukan farashin taki, Shettima ya ce a raba wa manoma Naira biliyan 250

Jirgin Air Peace a wani filin jirgin sama
Jirgin Air Peace a wani filin jirgin sama. Hoto: Air Peace
Source: Getty Images

Punch ta ce rahoton ya haifar da damuwa kan matakin tsaro a harkar jiragen sama, tare da jan hankalin kamfanonin su sanya ƙarin matakan kariya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda jirgin sama ya kusa hadari a Rivers

Tribune ta wallafa cewa NSIB ta bayyana cewa jirgin ya tashi daga Lagos zuwa Port Harcourt dauke da fasinjoji 103 da ma’aikatan jirgin.

Rahoton ya ce saukarsa bai yi daidai ba, inda ya taɓa ƙasa a mita 2,264 daga kusa da hanyar da ya kamata ya sauka, maimakon a cikin yankin da aka tsara.

Bayan haka, jirgin ya tsaya ne a mita 209 cikin filin da ke gefe, lamarin da aka ayyana da cewa kuskuren saukar jirgi ba bisa ƙa’ida ba.

An yi wa matukan jirgin gwajin giya

A cewar rahoton, sakamakon gwajin da aka yi wa matukan ya tabbatar da kasancewar sinadaran giya da wasu kwayoyi a jikin matukan.

NSIB ta bayyana cewa wannan na daga cikin abubuwan da ke tasiri wajen gudanar da aiki daidai, kuma hakan ya zama dalilin da zai iya haddasa irin hadarin.

Kara karanta wannan

Tinubu: Sai da rajistar haraji za a yi hulda da banki a Najeriya daga 2026

A shekarar 2006 aka kirkiro hukumar ta NSIB domin yin bincike irin wadannan.

An bukaci daukar matakin gaggawa

Hukumar ta NSIB ta ce duk da cewa babu wanda ya jikkata, amma sakamakon binciken ya tilasta musu su bayar da shawarwarin tsaro nan take ga kamfanin Air Peace.

Ta ce an umurci kamfanin ya ƙara tsaurara duba lafiyar matuka kafin jirgi ya tashi, da tabbatar da cewa ba a barin kuskuren da zai iya jawo barazana ga lafiyar fasinjoji da ma’aikata.

Binciken ya sake bude tattaunawa kan muhimmancin gwaje-gwajen lafiyar matuka a Najeriya, musamman ganin yadda mutane da dama ke dogaro da jiragen sama a tafiye-tafiyensu.

Jirgin Air Peace na kokarin tashi a filin jirgin sama
Jirgin Air Peace na kokarin tashi a filin jirgin sama. Hoto: Air Peace
Source: Getty Images

Masana harkar sufuri sun bayyana cewa dole ne a inganta tsauraran matakai, domin tabbatar da cewa dukkan jirage suna tafiya ne cikin yanayi mai cike da tsaro da aminci.

Jirgin sama ya yi hadari a Ghana

A wani rahoton, kun ji cewa an yi wani mummunan hadarin jirgin sama a kasar Ghana a watan da ya gaba.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Bako daga kasar waje ya yi mutuwar da ba a yi tsammani ba a Abuja

Hadarin ya hada da manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministoci, tsohon dan majalisa da wasu mutane.

Al'ummomi da dama a fadin duniya sun yi wa kasar Ghana jaje kan hadarin, ciki har da gwamnatin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng