Rikici da Dangote: NUPENG Ta Dauki Sabon Mataki da Zai Jawo Karancin Fetur a Najeriya

Rikici da Dangote: NUPENG Ta Dauki Sabon Mataki da Zai Jawo Karancin Fetur a Najeriya

  • Yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin NUPENG da matatar Dangote ta bi ruwa, inda yanzu sabon rikici ya barke tsakanin bangarorin
  • Sabuwar rigimar ta samo asali ne bayan Alhaji Sayyu Dantata ya ba direbobi umarnin cire tambarin NUPENG daga motocin MRS
  • NUPENG ta ce abin da Dantata ya yi ya saba doka, don haka ta dakatar da lodin mai a matatar, da barazanar sake shiga yajin aiki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Rikici ya sake barkewa tsakanin rukunin kamfanonin Dangote da ƙungiyar ma’aikatan mai da iskar gas ta ƙasa (NUPENG).

Wannan sabon rikici ya barke ne kwanaki bayan hukumar DSS ta jagoranci sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu, kan kungiyanci a matatar Dangote.

NUPENG ta dakatar da lodin fetur a matatar mai ta Dangote da ke Legas
Alhaji Aliko Dangote, da sababbin motoci masu amfani da CNG da Dangote ya sayo. Hoto: Dangote Group
Source: UGC

An dakatar da lodin mai a matatar Dangote

Rahoton Vanguard ya nuna cewa rikicin ya kunno kai ne bayan an umarci direbobin motocin mai na MRS da su cire tambarin ƙungiyar NUPENG da aka manna a motocinsu.

Kara karanta wannan

Rigimar ADC ta ki karewa, 'dan takarar shugaban kasa ya ce za a wargaza lissafin 'yan hadaka

Wannan mataki ya fusata shugabannin ƙungiyar NUPENG, inda suka dakatar da lodin mai a matatar Dangote da ke Lekki a ranar Alhamis.

A cewar wani jagoran ƙungiyar:

“Mun raba wa mambobinmu tambari bisa yarjejeniyar da aka cimma a hedikwatar DSS ranar Talata. Amma abin mamaki, bayan wasu sa’o’i muka ji an umarce su da su cire tambarin. Da muka dawo safiyar Alhamis, mun ga duk an cire tambarin. Wannan ya sabawa yarjejeniyar da aka yi.”

Shugaban ƙungiyar NUPENG, Williams Akporeha, ya tabbatar da barkewar sabuwar matsalar, yana mai cewa:

“Bayan yarjejeniyar da aka cimma a gaban ministoci uku da DSS, Alhaji Sayyu Dantata ya umarci direbobi su cire tambarin kungiya kuma su shiga matatar Dangote ta karfin tsiya. Mun hana su lodin mai saboda hakan ya sabawa dokokin NUPENG.”

An zargi jami'in Dangote da yin barazana

An ce Alhaji Sayyu Dantata, daraktan kula da harkokin sufuri a kamfanin Dangote kuma daraktan kamfanin MRS, ya jagoranci tawaga zuwa taron, wanda ya fara da misalin karfe 1:35 na rana, kuma ya kare da misalin karfe 7:15 na yammacin ranar Talata.

Kara karanta wannan

A karshe, Likitoci sun shiga yajin aiki, sun rufe asibitocin gwamnati baki daya

Sai dai, jaridar Daily Trust ta rahoto Williams Akporeha ya ce sun samu labarin Alhaji Dantata ya kira rundunar sojin ruwa domin murkushe jami’an ƙungiyarsu, lamarin da ya kira da "take doka".

"Alhaji Sayyu Aliyu Dantata ya yi shawagi a jami'anmu da jirgi mai saukar ungulu, sannan ya kira sojojin ruwa domin su murkushe jami'an kungiyar.
"Muna kira ga kowa da kowa, da a sanar da Alhaji Sayyu Aliyu Dantata cewa bai fi karfin doka ba. Muna Allah wadai da wannan halin nasa na girman kai."

- Williams Akporeha.

NUPENG ta dakatar da lodi a matatar Dangote bayan sabon rikici ya sake barkewa tsakaninsu.
Motocin dakon man fetur na kungiyar NUPENG a wani rumbun ajiyar mai a Legas. Hoto: @officialNUPENG9
Source: Depositphotos

NUPENG ta nemi daukin NLC kan Dangote

Shugaban NUPENG ya ce kungiyar za ta kare muradin 'yan Najeriya kuma ba za ta bari wani ya take doka don yana da kudi ba.

Williams Akporeha ya kuma umarci mambobin kungiyar NUPENG da su kasance cikin shirin sake shiga yajin aikin da aka dakatar.

Ya yi kira ga kungiyoyin kwadago, NLC, TUC, da sauran kungiyoyin farar hula da su fito domin nuna goyon baya a gare su.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, kamfanin Dangote Group bai fitar da wata sanarwa ba kan sabuwar takaddama da ta taso.

Kara karanta wannan

NNPCL: Mele Kyari ya yi magana bayan EFCC ta masa tambayoyi kan almundahana

Dangote zai fara raba mai kyauta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta bayyana shirinta na fara raba mai kyauta daga ranar Litinin 15 ga Satumba, 2025.

An tabbatar da cewa farashin mai ya sauka zuwa N841 a jihohin Kudu maso Yamma, yayin da a wasu jihohi za a sayar da lita a kan N851.

Wannan matakin na zuwa ne bayan tabbatar da isowar motocin CNG fiye da 1,000 don sauƙaƙa rarraba mai daga matatar Dangote zuwa jihohi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com