Albashin N70,000: An Gano Halin da Aka Jefa Ma'aikatan Kananan Hukumomi a Jihohin Arewa 3
- Ma'aikatan kananan hukumomi sun fara kokawa kan rashin aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 a wasu jihohi
- Kungiyar NULGE ta kasa ta bayyana cewa har yanzu ba a fara biyan mambobinta akalla N70,000 a Kaduna, Borno da Gombe ba
- Ta kuma koka kan yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da rike kudin kananan hukumomin jihar Osun, inda ta ce siyasa ce kawai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ana zargin har yanzu ma'aikatan kananan hukumomi ba su fara shan romon sabon mafi karancin albashi na kasa ba a jihohin Kaduna, Borno da Gombe.
Ƙungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE) ce ta yi wannan zargin, tana mai cewa gwamnatocin wadannan jihohi sun kasa fara biyan N70,000 ga mambobinta.

Source: Twitter
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Aliyu Kankara, ne ya bayyana haka bayan taron kwamitin zartarwa (NEC) na NULGE da aka gudanar a Abuja, Premium Times ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NULGE: Jihohi 3 sun gaza biyan N70,000
A cewarsa, jihohi da dama na biyan tsohon mafi ƙarancin albashi na ₦30,000 har yanzu, yayin da kaɗan ne suka fara aiwatar da sabon albashi na ₦70,000.
Aliyu Kankara ya ce:
“Daga cikin jihohin da ba sa biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan kananan hukumomi akwai Kaduna, Gombe da Borno.”
Shugaban NULGE ya ƙara da cewa mambobinsu a Kaduna sun bayar da wa’adin tafiya yajin aiki idan har ba a aiwatar da sabon albashi ba.
Kwamitin NEC na NULGE ya bayyana kin biyan sabon albashi a matsayin “zalunci da rashin adalci”, musamman ganin matsin halin tattalin arziki da ake ciki a ƙasar.
Sai dai kuma kungiyar ta yaba wa jihohin da suka yi gyara a tsarin albashinsu, musamman wadanda suka zarta adadin doka na N70,000.
NULGE ta soki matakin rike kudin Osun
Shugaban NULGE ya kuma soki matakin rike kudin kananan hukumomin jihar Osun, yana mai bayyana shi da cewa “siyasa ce kawai.”

Kara karanta wannan
'Sun fara kamfe a sakaye,' INEC ta fadi yadda 'yan siyasa su ke birkita mata lissafin 2027
Jaridar Guardian ta tattaro cewa duk da wannan matsala, Aliyu Kankara ya yaba wa gwamnatin Osun bisa yadda take iya biyan sabon albashi.
Ya bukaci gwamnatin tarayya ta saki kuɗaɗen da aka rike, yana mai gargadin cewa wannan matakin ba abu ne mai kyau ba kuma yan dakile ci gaba tare da ƙara jefa jama’a cikin wahala.

Source: Twitter
NULGE ta aika sako ga Bola Tinubu
Aliyu Kankara ya kuma tunatar da cewa duk da hukuncin kotun koli da ya bayar da ikon cin gashin kai ta fuskar kuɗi ga kananan hukumomi, babu wata ƙaramar hukuma a halin yanzu da ke karɓar kuɗinta kai tsaye daga tarayya.
Ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tilasta aiwatar da wannan hukunci, domin hakan zai ƙarfafa shugabanci a matakin ƙananan hukumomi.
Mafi karancin albashi ya kai N90,000 a Ebonyi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Ebonyi ya kara wa ma'ikata albashi, inda za a rika biyan N90,000 a matsayin mafi karancin albashi a jihar.
Gwamna Francis Nwifuru ya kara mafi karancin albashin ne a wani bangare na inganta walwala da jin dadin ma'aikatan gwamnati a Ebonyi.
Ya kuma tabbatar da cewa sabon mafi karancin albashi na N90,000 zai fara aiki nan take kuma ya shafi dukkan rukunan ma’aikatan gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

