Ganduje Ya Kafa Kwamiti, Zai Binciki Gwamnatin Kano kan Korar Kwamandojin Hisbah 44
- Tsofaffin kwamandojin Hisbah 44 na Kano sun kai ziyarar ban girma ga mataimakin shugaban majalisar dattawa a Abuja
- Sun shaida wa Barau Jibrin cewa gwamnatin Abba K. Yusuf ta kore su ne saboda kin shiga jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya
- Yayin da Sanata Barau ya fada masu abin da ke shirin faruwa, Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin bincike kan wannan kora da aka yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsoffin kwamandojin Hisbah daga kananan hukumomi 44 na Kano sun kai ziyarar ban girma ga mataimakin shugaban majalisar dattawa a Abuja.
Sun fada masa cewa, gwamnatin Kano, karkashin Abba Kabir Yusuf, ta kore su ne saboda sun ki shiga jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya.

Source: Twitter
A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a ranar Alhamis, Sanata Barau ya ce tawagar tsofaffin kwamandojin ta samu jagorancin Alhaji Ahmad Kadawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamandojojin Hisbah sun gana da Barau Jibrin
A yayin ziyarar, Alhaji Kadawa ya shaida wa Sanata Barau cewa:
“An kore mu ne saboda mun ki sanya jar hula, alamar tafiyar Kwankwasiyya. Mun zo ne mu sake jaddada goyon baya da biyayya gare ku da kuma jam’iyyar APC. Shirye-shiryen da kuka yi sun kara jawo kauna daga jama’a a Kano.”
Da yake martani, Sanata Barau ya nuna takaicinsa kan 'wulakancin' da gwamnatin Kano ta yi masu, inda ya shawarce su da su yi hakuri su dauki lamarin a matsayin jarrabawa daga Allah (SWT).
Ya kara da cewa:
“Da ikon Allah, lokaci zai zo da za a dawo da ku bakin aiki, kuma a biya muku dukkan hakkokinku.”
Ganduje ya kafa kwamitin binciken kora a Hisbah
A halin da ake ciki, tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa kwamitin mutum 44 domin tantance tsoffin jami’an Hisbah na Kano da aka ce gwamnatin Abba ta kora daga aiki.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun shiga uku, gwamna zai gina sabon sansanin sojoji na musamman a Kebbi
Shugaban kwamitin, wanda shi ne shugaban cibiyar NPC na kasa, Baffa Babba Dan Agundi, ya ce an ba su umarni su binciki lamarin, sannan su gano hanyoyin da za a iya dawo da jami’an da aka sallama.
Jaridar The Sun ta rahoto Baffa Dan Agundi ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan umarnin tsohon gwamnan Kano, Ganduje, inda ya kara da cewa korar jami’an Hisbah ta haifar da damuwa a tsakanin al’umma.

Source: Twitter
Ziyarar shugaban kwalejin noma ga Barau
Bayan taronsa da kwamandojin Hisbah, Sanata Barau ya kuma karɓi bakuncin sabon shugaban kwalejin fasahar noma ta tarayya da ke Kano, Dakta Salisu Salisu.
Sanata Barau ya bayyana jin dadinsa kan wannan nadin, yana mai cewa nadin ya dace da mutumin da aka nada.
Sanata Barau ya kara da cewa yana da yakinin cewa Dakta Salisu zai kawo gagarumin sauyi a kwalejin cikin manufar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hisbah ta hana saurarorin wakar Hamisu Breaker
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hukumar Hisbah ta Kano ta yanke hukuncin cewa wakar Amanata ta Hamisu Breaker, tana yada alfasha da kalaman batsa.
Ana zargin bidiyon da jarumar Kannywood, Khadija Mai Numfashi ta yi tana rangaji da lumshe idanu a kan wakar ya jawo fushin Hisbah.

Kara karanta wannan
Romon siyasa: Kansila ya naɗa sababbin hadimai 18, ya raba masu wurin aiki a Kaduna
Yayin da Hisbah ta haramta sauraron wakar, wasu sun fito sun nuna cewa matakin hukumar ya talla wakar ne kawai, don ba kowane ya santa ba da fari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
