Soyinka: Yadda Aka Sace Babban Marubucin Najeriya a Kasar Waje, Aka Yi Masa Fashi

Soyinka: Yadda Aka Sace Babban Marubucin Najeriya a Kasar Waje, Aka Yi Masa Fashi

  • Fitaccen marubucin Najeriya, Wole Soyinka ya ce an yi garkuwa da shi, kuma an yi masa fashi a babban birnin Romania
  • Wole Soyinka ya ce wani direban tasi ne ya sace shi lokacin da ya isa Romania don halartar taron baje kolin fasaha na Sibius
  • Marubucin ya ba da labarin yadda ta kaya tsakaninsa da direban, yadda ya tilasta shi shigar da bayan sirrin asusun bankinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Marubuci kuma wanda ya lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ba da labarin yadda wasu suka yi garkuwa da shi, suka kuma yi masa fashi.

Fitaccen marubucin, ya ce wannan iftila'i, mai ban al'ajabi da tsoratarwa, ya faru da shi ne a lokacin da ya kai ziyara birnin Bucharest, na kasar Romania.

An yi gurkuwa da fitaccen marubucin Najeriya, kuma aka yi masa fashi a Romania
Hoton fitaccen marubucin Najeriya, Farfesa Wole Soyinka. Hoto: @WSoyinkaCentre/X
Source: Twitter

Soyinka ya ba da labarin ne a wata hira da ya yi da jaridar TheNEWS, inda ya ce ya ziyarci kasar ne domin halartar babban bikin baje kolin fasahohi na Sibiu (FITS).

Kara karanta wannan

NNPCL: Mele Kyari ya yi magana bayan EFCC ta masa tambayoyi kan almundahana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bikin FITS, wanda ake yi a duk shekara a birnin Sibiu, na kasar Romania, yana samun halartar dubban masu fasaha da masu kallo daga ko'ina a duniya.

Yadda aka yi garkuwa da Wole Soyinka

Farfesa Wole Soyinka ya ce ya isa birnin Bucharest da misalin karfe 12:10 na dare, yana farin ciki zai halarci bikin FITS, amma sai abubuwa suka rikiɗe, lokacin da ya gaza haduwa da wanda aka ce zai zo ya dauke sa daga filin jirgin sama.

Bayan an yi sabanin, sai Soyinka ya yanke shawarar shiga tasi domin zuwa otel din Novotel, inda aka shirya zai sauka.

Ya ce maimakon direban ya nufi otel din, sai ya sauya hanya zuwa wani wuri da babu kowa, mai cike da duhu, inda aka tilasta masa bayar da bayanan asusun bankinsa.

"Bayan na shiga tasi, sai mutumin ya yi ta tafiya mai 'yar nisa, sannan ya kai ni wani wuri mai duhu, wanda babu alamar mutane a wajen.

Kara karanta wannan

Waye Larry Ellison? Makusancin shugaban kasa da ya fi kowa kudi yau a duniya

"Lokacin da muka je wajen, karfe 1:00 na dare ta yi. A nawa tunanin, mun tsaya ne saboda mun isa otel din, ashe ya sace ni ne. Nan fa ya fito da na'urar POS, ya ce na ba shi bayanan asusun bankuna na.."

An yi wa Wole Soyinka fashi da makami

Jaridar Daily Trust, ta rahoto wanda ya lashe kyautar Nobel din, ya ci gaba da cewa:

"In takaita maku zance dai, a nan ne na fahimci cewa garkuwa ya yi da ni, kuma yana son yi mun fashi, sannan ya jefar da ni a wannan wuri mai cike da ban tsoro.
"Dole na sanya lambar sirrina ba banki ta ba tare da ganin na'urar POS ba saboda mutumin ya rike ta. Yana ta nace mini 'ka sanya lambarka ta sirri, ka sanya lambarka ta sirri'."

A cewar Wole Soyinka, wannan takaddama ta dauki tsawon mintuna 25 zuwa 30, inda da gangan yake sanya lambar sirrin da ba dai dai ba, da tunanin ko wani zai zo ya kawo masa dauki.

"Na ci gaba da jan kafa, ina saka lambobi ba dai dai ba, ina ta addu'ar Ubangiji ya kawo wani, ko zai kawo mun dauki, amma sam, babu alamar mutane, ko irin masu shan sigarin nan babu."

Kara karanta wannan

Matashi ya yi tafiyar kilomita 600 don ya gana da gwamna, ya samu kyautar N10m

- Farfesa Wole Soyinka.

Wole Soyinka ya ce yana ji yana gani aka yi garkuwa da shi, kuama aka yi masa fashi.
Hoton fitaccen marubucin Najeriya, Farfesa Wole Soyinka. Hoto: @WSoyinkaCentre/X
Source: Twitter

Yadda ta kaya tsakanin Soyinka da dan fashi

Wole Soyinka ya ce har sai da aka fitar da shi daga cikin motar ne ya fahimci cewa a bayan gari suke, amma har a lokacin, yana fatan wani zai biyo sahu, don kawo masa dauki.

Saboda yadda yake jan kafa kan sanya lambobin sirrinsa, Soyinka ya ce dan tasin ya fara tunanin ko shi wani babba ne, da yake tunanin za a kawo masa dauki.

"Na shiga wani yanayi maras dadi, ina ji ina gani, aka yi garkuwa da ni, kuma aka yi mani fashi. Amma dai a karshe, na isa otel din a cikin wannan dare. Wata motar ce ta zo ta dauke ni zuwa Sibiu."

- Wole Soyinka.

Wole Soyinka ya mika bukata ga Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Farfesa Wole Soyinka ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya binciki mutuwar Dele Giwa, Kudirat Abiola da Bola Ige.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Lauyan Sowore ya nemi su hadu a kotu da Tinubu

Fitaccen marubucin yake cewa akwai wadanda Tinubu ya ba lambar yabo a ranar Dimokuradiyya ta 2025, wadanda suka cancaci a yi bincike kan mutuwarsu.

Har ila yau, ya yabawa karramawar da aka yi wa jaruman yaki da mulkin soja, amma ya ce akwai wasu muhimman sunaye da Tinubu ya manta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com