'Ya Aikata Laifuffuka 2,' Gwamna Nasir Idris Ya Dakatar da Kwamishinan Lafiya
- Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kebbi, Yunusa Isma'il ya gamu da fushin Gwamna Nasir Idris kan watsi da damar da aka ba shi
- A yammacin ranar Alhamis, 11 ga Satumba, 2025, gwamnatin Kebbi ta sanar da dakatar da kwamishinan, bisa umarnin gwamna
- Kauran Gwandu ya umarci kwamishinan da ya ba da hujja mai karfi da za ta hana daukar karin matakan ladabtarwa a kansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya dakatar da kwamishinan lafiya na jihar, Yunusa Isma’il.
An dakatar da dan majalisar zartarwar ne bisa zarginsa da sakaci da rashin aiwatar da ayyukan da aka dora masa yadda ya dace.

Source: Facebook
Gwamna ya dakatar da kwamishinan lafiya
A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya fitar ranar Alhamis, an ce dakatarwar ta fara aiki nan take, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Nasir Idris ya umarci kwamishinan da ya bayar da hujja mai karfi kan dalilin da zai hana daukar karin matakan ladabtarwa a kansa.
Sanarwar ta kara da cewa,
"Mai girma gwamna ya umurci kwamishinan lafiya da aka dakatar da ya gabatar da dalilin da zai hana daukar karin matakan doka a kansa, domin ya yi watsi da amanar da aka ba shi."
Gargadin gwamna ga jami'an gwamnati
Matakin dakatar da kwamishinan lafiyar, ya biyo bayan alkawarin da Gwamna Nasir Idris ya dauka na ladabtar da duk jami'in gwamnati da ya yi sakaci da aikinsa.
Gwamnatin Nasir Idris ya sha nanata wa mukarraban gwamnati muhimmancin rikon gaskiya, ladabi da jajircewa a cikin hidimar jama’a.
Dakatarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun karin sukar gwamnati kan tabarbarewar tsarin kula da lafiyar al'umma a jihar Kebbi, inji rahoton Punch.
'Dan jarida ya fallasa tsarin kiwon lafiya
Kwanan nan, wani ɗan jarida, Hassan Mai-Waya Kangiwa, ya shiga hannun jami'an tsaro bayan ya wallafa wani bidiyo da ya karade intanet.

Source: Twitter
A cikin bidiyon, dan jaridar ya nuna yadda marasa lafiya a asibitin Kangiwa suke kwance a kan gadon karfe babu katifa.
Bidiyon ya haifar da ce-ce-ku-ce mai zafi a shafukan sada zumunta da kuma cikin gari, wanda aka ce ya tilasta gwamnati yin bincike kan yadda ake gudanar da asibitoci a jihar.
A baya bayan nan, an samu gwamnonin da suka dakatar da kwamishinoninsu a 2025; karanta wasu labarai makamantan wannan a kasa:
Wasu labarai game da dakatar da jami'an gwamnati
Gwamna ya gano badaƙalar kudi, ya dakatar da kwamishina da shugaban hukuma
Gwamna ya dakatar da kwamishinoni 25 da wasu hadimai 60 a Ebonyi
Gwamna Francis Nwifuru ya dakatar da kwamishinoni daga aiki
Gwamna bago ya kori dukkan kwamishinoni
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Umaru Bago, ya amince da korar dukkan kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin Neja.
Sai dai, wannan korar ba ta shafi shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, mataimakinsa, sakataren gwamnatin jihar da manyan jami’an fadar gwamnati ba.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun shiga uku, gwamna zai gina sabon sansanin sojoji na musamman a Kebbi
A shekarar 2023 ma gwamnan ya dauki irin wannan mataki na rushe hukumomi, kwamitoci da kuma cire masu rike da mukaman siyasa a jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

