A Karshe, Kotun Abuja Ta Yanke Hukunci kan Shugaban Kungiyar Ansaru da Aka Cafke
- Wata Kotu da ke zamanta a birnin Abuja ta yanke hukunci kan wasu daga cikin kwamandojin kungiyar Ansaru da aka kama kwanakin baya
- Kotun ta yanke wa Mahmud Usman, kwamandan Ansaru, hukuncin shekaru 15 bayan ya amsa laifin ma’adinai ba bisa ka’ida ba
- Mai shari’a Emeka Nwite ya ba da umarnin a tsare shi har zuwa shari’ar sauran tuhume-tuhume 31, inda aka dage zuwa Oktoba 21
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ta yi zama domin yanke hukunci kan kwamandan kungiyar Ansaru.
Kotun ta yanke wa kwamandan, Mahmud Usman, hukuncin daurin shekaru 15 a gidan gyaran hali bayan samun shi da laifuffuka da suka shafi ta'addanci.

Source: Facebook
An gurfanar da 'dan kungiyar Ansaru a kotu
Rahoton Channels TV ta ce hukuncin ya biyo bayan cafke wasu daga cikin kwamandojin Ansaru wanda Usman na cikinsu.

Kara karanta wannan
Sanata Ndume ya 'gano' makircin masu kiran a kori hafsoshin tsaro, ya gargadi Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar DSS ce ta gurfanar Usman, wanda ya amsa laifin hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da aka ce ya taimaka masa wajen samun makamai don ta’addanci da satar mutane.
Mai shari’a Emeka Nwite ya ba da umarnin a tsare shi a hannun DSS har zuwa shari’ar sauran tuhume-tuhume 31 da ake masa.
Wace tuhuma ake yi wa 'dan Ansarun?
A cikin tuhume-tuhume 32, an zargi Usman da Abubakar Abba da kai hari Wawa Cantonment na Sojojin Najeriya a Kainji, Niger a 2022.
An ce harin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, tare da samun horo kan makamai da kera abubuwan fashewa daga sansanonin ta’addanci daban-daban.
Haka kuma, an ce sun samu horo kan dabarun yaki daga wata ƙungiyar ta’addanci a Mali, kafin kotu ta dage shari’a zuwa Oktoba 21.
DSS ta zargi shugabannin da kitsa harin gidan yarin Kuje a 2022, wanda ya kubutar da sama da fursunoni 600 a lokacin.

Source: Facebook
Sauran zarge-zarge da ake yi ga Ansaru
An kuma ce sun shirya kai hari kan wurin hakar ma'adinan uranium a Niger da garkuwa da Faranshi Francis Collomp a 2013, da sauran manyan laifuffuka, cewar rahoton Punch.
Nuhu Ribadu ya tabbatar da kama su, yana mai cewa an samu nasarar hakan ne bayan hadin gwiwar jami’an tsaro, inda ya bayyana Usman a matsayin jagoran Ansaru.
Ya ce Mamuda ya kasance yana jagorantar “dakin da ake kulle mutane da ake kira "Mahmudawa” a kusa da Kainji National Park, yayin da Ansaru ta samo asali a Kano a 2012.
Jami'an tsaro sun damke 'Yan Ansaru
A makonnin baya ne rahoto ya gabata cewa Gwamnatin Najeriya ta sha yabo bayan kama shugabannin 'yan kungiyar ta'addan Ansaru a kasar.
Amurka ta yaba da nasarar tare da kara karfafa jami'an tsaron Najeriya ganin wannan gagarumar nasara da aka samu a yaki da ta'addanci.
Haka zalika Birtaniya ta yaba da kokarin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu wajen kama 'yan ta'addan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

