Budurwa Ta Mutu a Ɗakin Saurayinta a Abuja, Ƴan Sanda Sun Cafke Wanda Ake Zargi
- A wani yanayi mai cike da rikitarwa, an tsinci gawar wata budurwa 'yar shekara 24 a gidan saurayinta da ke Gwagwalada, Abuja
- Rahotannin farko sun nuna cewa an gano wasu magunguna a dakin da ta mutu, amma babu alamar rauni jikin marigayiyar
- Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaro sun cafke saurayinta, yayin da suke kokarin binciko gaskiyar abin da ya jawo ajalin budurwar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An sake samun wani mummunan lamari a Abuja bayan wata budurwa mai shekara 24 da haihuwa, Kelechi Ebubechukwu, ta mutu a dakin saurayin da za ta aura.
An rahoto cewa, an tsinci gawar Kelechi Ebubechukwu a dakin saurayin nata ne da ke Gwagwalada, kuma ana kyautata zaton ta mutu ne a ranar Talata.

Kara karanta wannan
Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba

Source: Twitter
Budurwa ta mutu a dakin saurayinta
A ranar Laraba ne labarin mutuwar Kelechi ya bazu, bayan da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa rahoton mutuwar a shafinsa na X.
Mai sharhin ya ruwaito daga majiyoyin ‘yan sanda cewa binciken farko ya nuna marigayiyar tana fama da zazzabin cizon sauro kafin ta riga mu gidan gaskiya.
An kuma gano magungunan da ake kyautata zaton na cutar zazzabin cizon sauro ne a dakin da aka tsinci gawar budurwar.
Duk da haka, babu wata alamar rauni ko shan wuya a jikinta, lamarin da ya sa ake kallon cutar ce ta zama sanadin mutuwarta, ba wai kashe ta aka yi ba.
'Yan sanda sun cafke saurayin budurwar
A halin da ake ciki, majiyoyin tsaro sun ce an cafke saurayin marigayiyar, sannan an tsare shi domin gudanar da bincike yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin gano hakikanin abin da ya faru.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro da ƴan bindiga sun gwabza ƙazamin faɗa a Malumfashi, an rasa rayuka
Mutuwar ta jawo hankalin jama’a saboda karuwar mace-macen mata a dakunan samarinsu a Najeriya, a cewar rahoton jaridar Punch.
Yadda ake samun gawar masoya a dakuna
Rahotanni 'yan sanda sun sha nuna cewa matan kan mutu ne yayin jima'i, yayin da wasu mace-macen ake dangantasu da rikice-rikicen cikin gida ko matsalolin rashin lafiya.
Wannan matsala ba ta tsaya ga iya mata ba, domin an sha samun labaran maza, musamman masu aure, sun mutu a dakin otel yayin saduwa da 'yan matansu.
Haka zalika ana alakanta wasu mace-macen da harkokin tsafi da ake yi da mutane.

Source: Twitter
Labarin mutuwar 'yan mata a dakunan samarinsu
Karanta wasu labarai kan mutuwar 'yan mata a gidajensu samarinsu a kasa:
An tsinci gawar dalibar jami'ar UNIPORT a dakin saurayinta
Daga zuwa kwanan gida an tsini gawar wata budurwa a dakin saurayinta
Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta
Yadda wata mata ta mutu bayan kammala zina da saurayinta dan sanda
An tsinci gawar wata mata mai juna biyu da Saurayinta a cikin daki

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Malami ya mutu yana lalata da dalibarsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani babban malamin jami'ar PAAU da ke jihar Kogi, Dr. Olabode Ibikunle, ya mutu yana lalata da dalibarsa a otel.
Binciken jami'an tsaro ya nuna cewa an malamin ya sha magungunan kara kuzarfi, wanda ake zaton su ne silar mutuwarsa lokacin da yake jima'i.
Rundunar ’yan sandan Kogi ta ce an gudanar da binciken gawa, kuma an kama ɗalibar da suka yi lalata tare malamin dongudanar da ƙarin bincike.
Asali: Legit.ng